Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya bukaci a zage damtse wajen kafawa, da aiwatar da tsarin aiki, karkashin ka’idar nan ta “Muhalli mai kyau zai haifar da alfanu da bunkasa tattalin arziki”, tare da bude sabon babin gina wayewar kai ta fuskar kare muhallin halittu a sabon zamani.
Li, ya yi tsokacin ne yayin bude bikin ranar kare muhallin halittu ta kasa, taron da ake fatan amfani da shi wajen tattauna yadda za a aiwatar da manufar a zahiri. Ya ce, tattalin arzikin kasar Sin, da bunkasar zamantakewar kasar, sun shiga wani sabon mataki na ci gaba mai inganci, ta yadda ake gaggauta sauya turba zuwa samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, da fitar da mafi karancin iskar carbon mai dumama yanayi, kuma wajibi ne a nacewa hanyar daukaka matsayin kare muhallin halittu da neman ci gaba marar gurbata yanayi.
Firaminista Li Qiang ya kara da cewa, “Ya kamata mu ingiza sauyi a fannin masana’antu zuwa marasa gurbata muhalli, da masu fitar da karancin iskar carbon, da gaggauta kafuwar tsarin masana’antu masu kunshe da fasahohi masu inganci, da karancin amfani da albarkatu, da karancin gurbata muhalli. Kazalika, ya dace mu ingiza kafuwar tsarin wayewar kai a fannin kare muhallin halittu a matakin kasa da kasa, da hada hannu da dukkanin sassa, wajen ingiza kare muhallin halittu, da shawo kan kalubalen sauyin yanayi, da hadin gwiwar wanzar da ci gaban duniya mai dorewa. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp