Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya gana a yau Litinin da darakta janar ta hukumar kula da cinikayya ta duniya WTO, Ngozi Okonjo Iweala, a birnin Tianjin na kasar Sin.
Yayin ganawar, Li Qiang ya ce Sin ta shirya aiki da dukkan bangarori domin goyon bayan tsarin huldar kasa da kasa da cinikayya cikin ‘yanci da kare halaltattun hakkoki da muradun kasashe masu tasowa. A nata bangare, Ngozi Iweala ta ce tun bayan shigarta kungiyar WTO, kasar Sin ta ci gaba da inganta bude kofa da mara baya ga tsarin cinikayya tsakanin kasa da kasa, kuma ta cimma nasarori ta fuskar ci gaba.
Har ila yau, Li Qiang ya gana a yau din da shugaban dandalin tattauna tattalin arzikin duniya, Klaus Schwab, inda ya bayyana cewa a shirye kasar Sin take ta hada hannu da dukkan bangarori wajen ci gaba da gina tattalin arzikin duniya mai adalci. A nasa bangare, Schwab ya ce dandalin ma ya shirya zurfafa hadin gwiwa da kasar Sin. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha)