Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya bukaci kara azamar gudanar da manyan ayyukan kasa a babban mataki na inganci, da sa kaimi ga bunkasar tattalin arziki da zamantakewa, da kyautata jin dadin jama’ar kabilu daban daban.
Li ya bayyana hakan ne a yayin ziyarar gani da ido da ya kai daga ranar Jumma’a zuwa Asabar a yankin Xizang mai cin gashin kansa da ke kudu maso yammacin kasar Sin. A yayin rangadin, ya jaddada bukatar ba da fifiko wajen kiyaye muhalli, da tabbatar da aiwatar da manyan ayyuka na kasa, da samar da masana’antu na musamman masu fafata gasa wadanda suka dace da yanayin cikin gida.
Yayin da yake duba aikin gina layin dogo na Sichuan zuwa Xizang a birnin Nyingchi, Li ya ce, kammala aikin layin dogon tare da kaddamar da shi zai kasance mai matukar muhimmanci ga bunkasa ci gaban Xizang da inganta rayuwar jama’a, yana mai cewa, dole ne a tabbatar da inganci da kiyaye hatsari su kasance kan gaba a koyaushe.
A wani yanki na gwajin noma na zamani a Lhasa, babban birnin Xizang, Li ya ga yadda ake bunkasa ayyukan noma da kiwo na Xizang da kuma cibiyar masana’antun kiwon dabbobi da kuma tsangayar nazarin halittun kan-tudu. Ya bayyana cewa, amfani da albarkatun gida na musamman don bunkasa aikin gona da kiwo na kan-tudu ya zama wata babbar hanyar samun kudin shiga ga jama’a da kuma karfafa ci gaban tattalin arziki a Xizang. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp