A yau ne, firaministan kasar Sin Li Qiang, ya jagoranci taron majalisar gudanarwar kasar, inda ya saurari rahoton yadda ake tafiyar da shawarwarin wakilan majalisar wakilan jama’ar kasar Sin, da shawarwarin wakilan majalisar ba da shawara kan harkokin siyasar Sin a bara.
Taron ya yi nazari kan matakan jawo hankali da amfani da jarin waje da kara himma da shirya ayyukan katsewa da dakile hadurran bashi na cikin gida.
Taron ya kuma amince da wasu muhimman takardu na gwamnati, ciki har da tsari kan kara inganta ayyukan biyan kudi da kuma kara saukaka hanyoyin biyan kudi. (Yaya)