Firaministan kasar Sin Li Qiang ya jagoranci taron majalisar gudanarwar kasar Sin, wanda ya amince da shirin aiwatar da ayyukan raya amfani da makamashi mai tsafta a bangaren masana’antu na shekarar 2025 zuwa ta 2027, tare da sake duba matakan da za a dauka na inganta tsarin biyan diyya domin kiyaye lafiyar muhalli.
Taron ya jaddada bukatar hanzarta yin kirkire-kirkire na fasahohin makamashi mai tsafta da kuma fadada hanyoyin samar da mafita, yayin da ake kiran gudanar da gagarumin sauyi mai zurfi a bangaren tsoffin masana’antu.
Har ila yau, ya bukaci sassa masu tasowa da su ci gaba da samar da ingantaccen ci gaba wajen amfani da makamashi mara gurbata muhalli tun daga tushe, tare da mai da hankali kan inganta samar da makamashi mai tsafta da kayayyakin da suka jibanci haka, da kuma daga darajar matakin sake sarrafa albarkatu da amfani da su.
Har ila yau, taron ya nemi a ci gaba da habaka samar da hanyoyin biyan diyya a sassan da ke manyan koguna, yayin da ake ci gaba da fadada tsarin da aka kebe don ya hada da sauran abubuwan da suka shafi muhalli kamar dazuzzuka, da filayen ciyayi, da kuma yanayi. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp