Firaministan Sin Li Qiang, ya ce kasar Sin a shirye take ta karfafa daidaita dabarun samar da ci gaba tare da sassa daban daban, da daga matsayin bude kofofi da hadin gwiwa, da ci gaba da ingiza damammakin bunkasa tattalin arziki, ta yadda za a iya lalubo karin fagagen samar da ci gaba.
Li Qiang, ya yi tsokacin ne a jiya Litinin, yayin taro karo na 28 na “ASEAN Plus Three” da aka bude a kasar Malaysia. Firaministan na Sin ya kara da cewa, cikin gwamman shekaru, a matsayin daya daga cikin yankuna mafi saurin samun ci gaba a duniya, gabashin Asiya na ci gaba da shaida nasarorin tattalin arziki masu ban mamaki. Kuma bude kofa, da hadin gwiwa abubuwa ne masu kima, wadanda aka gano, tare da killace su ta hanyar kwarewa, kana ya kamata a martaba da yin tafiya tare da su a ko da yaushe, ta yadda za su kasance muhimman alfanu, kuma jigon cimma nasarar raya tattalin arzikin yankin na gabashin Asiya.
Har ila yau, Li ya jaddada cewa, abubuwan ban mamaki da yankin ke shaidawa ba su kare ba, domin za su ci gaba da gudana ba yankewa. Daga nan sai ya yi kira ga sassa masu ruwa da tsaki, da su samar da wani yanayi mai kyau na bunkasa yankin. Ya ce domin cimma cikakkiyar nasarar kare zaman lafiya da daidaito, wanda aka samu ta hanyar aiki tukuru a yankin na gabashin Asiya, kamata ya yi a kara azamar warware sabani ta hanyar gudanar da tattaunawa da shawarwari, da goyon bayan cinikayya cikin ‘yanci, da kare tsarin cudanyar mabanbantan sassa, da nuna adawa ga dukkanin akidu na kariyar cinikayya, da ingiza dunkulewar tattalin arzikin shiyyar sannu a hankali. (Saminu Alhassan)













