Ma’aikatar harkokin wajen Sin ta sanar a yau Alhamis cewa, firaministan kasar Li Qiang, zai halarci bikin rufe gasar wasannin lokacin hunturu ta kasashen Asiya karo na 9, wanda za a yi gobe Juma’a a Harbin, babban birnin lardin Heilongjiang na kasar Sin.
Li Qiang zai kuma shirya liyafar maraba da shirye shiryen da suka shafi huldar kasa da kasa ga shugabannin kasashen waje da za su halarci bikin rufe gasar. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)