Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce a jibi Alhamis 4 ga watan nan, firaministan kasar Sin Li Qiang, zai halarci bikin bude babban taron fasahohin kwaikwayon tunanin bil adama ko AI na kasa da kasa na 2024, da taron manyan jami’ai game da jagorancin fasahohin AI na kasa da kasa, inda kuma zai gabatar da jawabi. (Mai fassara: Saminu Alhassan)