Firaministan kasar Sin Li Qiang, zai halarci taron kasa da kasa na manyan jami’ai, game da jagorancin fasahar kirkirarriyar basira ko AI a matakin kasa da kasa.
A cewar kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Guo Jiakun, Li Qiang zai gabatar da jawabi yayin taron na AI na bana, wanda zai gudana a birnin Shanghai a ranar Asabar 26 ga watan nan na Yuli.
- Xi Ya Bukaci Sin Da EU Su Samar Da Kwanciyar Hankali Da Tabbaci Ga Duniya
- Xi Ya Bukaci Sin Da EU Su Samar Da Kwanciyar Hankali Da Tabbaci Ga Duniya
Guo Jiakun ya ce, taron zai kasance muhimmin mataki da Sin za ta aiwatar, a fannin jagorancin fasahar AI, bayan da shugaba Xi Jinping ya gabatar da shawarar hakan, zai kuma kasance dandalin jagorancin fayyace fasahohi, da baje manhajoji, da ingiza bunkasar masana’antu, tare da zamowa majalisar jagoranci a fannin na AI.
Guo Jiakun ya kara da cewa, jigon taron na bana shi ne goyon bayan kasashen duniya a zamanin fasahar AI. Kuma Sin ta gayyaci manyan wakilai daga kasashe da hukumomin kasa da kasa sama da 40 zuwa taron na bana.
Kazalika, Sin na fatan karfafa goyon baya, da hada karfi don samar da ci gaba, da aiki tukuru wajen bunkasa fasahar AI bisa inganci da kyakkyawan tsari, tare da tabbatar da hakan ya zama karfi mai nagarta, da tsaro da adalci. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp