A cikin wata hira da wakiliyar CMG, firaminstar Barbados Mia Amor Mottley ta ce, Barbados za ta ci gaba da taka rawar gani cikin shirin gina shawarar “ziri ɗaya da hanya ɗaya”. Ta ce, shawarar da kasar Sin ta gabatar ya yi daidai, wadda ba wai tana sa kaimi ga cudanya a duniya kadai ba, har ma tana samar da sabbin damammaki ga kasashe.
Ta ce, Barbados ba ta taba yin shakku kan ingancin hadin gwiwar da ke tsakaninta da kasar Sin ba, kasancewar kasar Sin abokiyar ci gaban Barbados tun bayan samun ‘yancin kai.
Motley ta kuma bayyana cewa, rikicin duniya ya jefa wasu kasashe cikin hadarin fadawa cikin talauci. A yayin da ake tinkarar wannan batu, duniya na bukatar kwarewar kasar Sin. Ta ci gaba da cewa, a wannan duniyar da muka shagaltu da samun moriyar nan da nan, wayewar kan kasar Sin da ci gabanta sun shaida mana cewa, samun hangen nesa shi ne abu mafi muhimmanci. (Mai fassara: Yahaya)