Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya halarci taron mataki na 2 da na 3 na ganawar shugabannin BRICS karo na 17 da aka gudanar a Rio de Janeiro hedkwatar kasar Brazil, tsakanin ranakun 6 zuwa 7 ga watan nan da muke ciki, tare da gabatar da jawabi.
Li ya ce, hadin gwiwar kasashen BRICS dole ne ya nace ga matsayin kiyayewa da tabbatar da cudanyar bangarori daban-daban a duniya, da gaggauta kafa tsarin ciniki da tattalin arzikin duniya mai adalci da bude kofa, da hada kan kasashe masu tasowa, don taka rawar gani ga samun bunkasar duniya mai dorewa.
Ya kara da cewa, ya kamata a dukufa kan shimfida halayen tattalin arzikin duniya mai bude kofa, da daga matsayin hadin gwiwar kasa da kasa kan harkar hada-hadar kudi, da ma bullo da wata sabuwar hanyar samun bunkasar tattalin arziki. A nata bangare, Sin za ta samar da abun koyi dangane da hadin gwiwar yanar gizo tsakanin kasashe masu tasowa karkashin shawarar raya duniya, don gabatar da ayyukan ba da horo har 200 ga kasashe masu tasowa a shekaru 5 da suke tafe, a bangaren tattalin arzikin yanar gizo, da fasahar AI da sauransu.
Li ya kuma jadadda cewa, dole ne al’ummun duniya su hada hannunsu wajen tinkarar sauyin yanayi, da kara samun ingantaccen ci gaban kiyayen muhallin hallitu, da gaggauta karfin gudanar da ayyukan kiwon lafiyar jama’a. Kuma Sin za ta ci gaba da daukar nagartattun matakai, da sauke nauyin dake wuyanta, na kokarin ciyar da hadin gwiwar mabambantan bangarori don samun bunkasa mai kiyaye muhalli a dogon lokaci. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp