Fim din na kagaggun hotuna na kasar Sin da ya kafa tarihi mai suna “Ne Zha 2” ya dire matsayi na 7 a jerin manyan fina-finan duniya mafi samun kudi, inda yawan kudin shiga da aka samu daga kallonsa ya zarce na “Spider-Man: No Way Home”, a cewar dandalin sayar da tikitin kallon fina-finai a yau Asabar.
Wannan fim din ya shiga jerin fina-finai 10 mafi samun kudi a duk duniya a ranar 17 ga watan Fabrairu, wato kwana na 20 bayan nuna shi a ranar 29 ga watan Janairu, wanda ya kasance a lokacin bikin Bazara na al’ummar Sinawa ta shekarar 2025.
- Ma’aikatar Tsaron Jama’ar Sin Na Matukar Adawa Da Barazanar Da Amurka Ta Yi Na Karin Haraji
- Xi Ya Jaddada Ciyar Da Shirin Kasar Sin Mai Kwanciyar Hankali Zuwa Babban Mataki
Ya zuwa karfe 1 da minti 50 na rana na yau Asabar, yawan kudin da aka samu na “Ne Zha 2” a duniya, ciki har da na yin odar tikiti kafin a kallo wato presale, ya zarce yuan biliyan 14.2, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 1.98, a cewar bayanai daga dandalin sayar da tikiti na Maoyan.
Wannan ci gaba na daya daga cikin jerin nasarori masu ban sha’awa. Fim din na “Ne Zha 2″ ya riga ya zama fim na farko da aka samu sama da dalar Amurka biliyan 1 a kasuwa guda, kuma shi ne fim din da ba na Hollywood ba, da ya fara shiga cikin rukunin fina-finan da yawan kudaden da aka samu daga kallonsu da ya kai dalar Amurka biliyan 1. Har ila yau, ya tumbuke fim din kamfanin Disney na shekarar 2024 mai suna ” Inside Out 2″, ya zama fim din na kagaggun hotuna da aka fi samun kudi daga kallonsa a kowane lokaci a duniya. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp