- Yadda Tsoro Da Kunya Suka Lullube Ni Farkon Shigata Fim
- Masu Son Shiga Fim Su Nemi Izinin Iyaye, Su San Hannun Wa Za Su Fada
- Yadda Na Tsinci Kaina A Shirin Labarina Da Na Kwana Casa’in
Daya daga cikin fitattun jaruman da ke haskawa a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, da ke taka rawa matsayin Uwa a cikin shiri mai dogon zango na Labarina wato RAHAMA SIDI ALI, ta bayyana irin kalubalen da ta fuskanta yayin fara daukar shirin Labarina da kuma irin kallon da mutane ke mata sakamakon fitowarta a matsayin Uwa a fim har ma da wasu batutuwan masu yawa. Ga dai tattaunawar tare da wakiliyarmu RABI’AT SIDI BALA Kamar haka:
Da farko za ki fara da fada wa masu karatu cikakken sunanki da takaitaccen tarihinki.
Sunana Rahma Sidi Ali. Ni haifaffiyar garin Kaduna ce, a Kaduna na taso a Kaduna na yi duk wata rayuwata. An haife ni 22/7/1989, na yi firamare da sakandare a Kaduna daga nan na je ‘Polytechnic’ Kaduna, Allah bai sa na gama ba, a takaice kenan.
Ya batun iyali, shin akwai ko babu?
Gaskiya a yanzu dai babu, amman ina fatan in sha Allahu zan samu nan gaba.
Idan na fahimce ki, kina so ki ce baki taba aure ba, ko ya kike nufi?
A’a! Na taba aure Allah ne dai bai ba ni haihuwar ba, amma na taba aure.
Me ya ja hankalinki har ki ka tsunduma cikin masana’antar kannywood?
Gaskiya tun ina karama nake sha’awar harkar fim, na taso ina sha’awar abun kuma ina burin yinsa, dan bana mantawa kafin nayi aure lokacin ina da kawa ana ce mata Balaraba Ubangiji Allah ya ji kanta yanzu ta rasu, ita ta fara ja na shagon Yakubu Lere muna dan zuwa, a gida ma ba a san muna zuwa ba sabida muna sha’awar abun. Bayan na yi aure kin san an ce aure rai gare shi da Allah ya sa na rabu da mijina sai na ga ‘why not’ tun da ina sha’awar fim bari na shiga harkar fim yana burge ni, abin da ya ja hankalina kenan sabida ina so.
Ya gwagwarmayar shiga cikin masana’antar ta kasance?
Alhamdu lillah Ala Kulli halin, gaskiya ba abin da zan ce sai dai Alhamdu lillahi. Saboda ni ban samu irin wannan gwagwarmayar da wasu suke fadin sai ka sha wahala sai ka yi ka-za, gaskiya ni ban same shi ba. Na shiga harkar fim cikin sauki cikin kwanciyar hankali, Alhamdu lillah ban samu wadannan matsalolin ba.
Mutane da dama sun fi sanin ki a cikin shirin Labarina, shin daman can kina fim ne ko kuwa shi ne fim dinki na farko da ki ka fara fitowa ciki?
A’a! Gaskiya na yi finafinai da bai wuce irin guda uku zuwa hudu ba, fim dina na farko shi ne ‘Farar Mace’, fim din wani bawan Allah da ake ce mishi Dansudan a Kaduna, shi ya fara yi mun fim Farar Mace, kuma ni na jagoranci fim din. Sannan na zo na fito a ‘Matar Abokina’, shi ma na zo na yi ‘Kwana Casa’in’, ina fitowa a kwamishinar mata, su kenan finafinan da na yi sai ‘Labarina’.
Za ki yi kamar shekara nawa da fara fim?
Eh! To, ‘i think’ daga farawata zuwa yanzu zan yi shekara shida.
Ya a ka yi kika tsinci kanki a cikin shirin labarina, har ma da kwana casa’in?
Bari na fara da Kwana Casa’in, wani ‘causing’ dina ne muna zaune da shi na ce mishi ina son Dadin Kowa na Arewa24, sai ya ce mun ai akwai wanda ya sani a Arewa24 Aminu kenan wanda ya ke yin shirin Top 10, sai ya kira shi ya ke yi masa magana, sai ya ce yana umrah idan ya dawo zai wa furodusan magana yadda ake ciki za a neme ni. Yana dawowa kuwa ya yi wa furodusan magana aka neme ni na je Arewa24 suka dan yi mun ‘yan tambayoyi haka na yi signing. Aiki na zuwa sai suka kira ni da suka kira ni har ga Allah a lokacin sai na ji kamar ma ba na son in yi fim din, na rika kame-kame a haka dai, sai mutumin ya sake kira na ya ce mun Rahama kina son aikin nan ko ba kya so? Na ce masa ina so sai suka turo mun kudin mota dan ba na mantawa da yamma na tafi Jigawa na yi shigar dare, ina shiga lokacin ma aka fara aiki.
Labarina kuma gaskiya ni na nema da kaina, ni na sa aka ba ni lambar Malam na yi mishi magana a Whatsapp tun labarina na farko na su Sumayya kenan, na ce masa ina so, a lokacin ma bai ma ba ni amsa ba, kawai ina zaune dai wani dan lokaci kamar wata daya zuwa wata biyu sai Yunusa Mu’azu ya kira ni da yake na san shi mun yi aikin kwana casa’in da shi, da ya kira ni sai ya ce mun “Rahama har yanzu kina harkar fim?” sai na ce masa Eh, sai ya ce “Tohm za mu yi aiki da ke” sai na ce wane irin aiki ne? Sai ya ce “Labarina” sai na ce a ina ne? Sai ya ce a Gombe ne za a yi, sai na ce masa to, ba matsala. Lokaci na zuwa sai Dan Ma’azu ya kira ni ya ce mun jibi zan shigo, na ce masa ba matsala, kin ji yadda aka yi na tsinci kaina a Labarina.
Ya farkon farawarki ya kasance?
Kai..! [Dariya], gaskiya farkon farawata, na shiga rudani da dan damuwa, saboda rol ne na gani babba zan fito a Uwa a matsayin Mamar Maryam, da aka bani sai na fara tunanin ya zan yi na yi aktin din Uwa?, ban mantawa sai Asma’u Sani, daki daya muke da ita, ita ce ta fara ba ni kwarin gwiwa a kan na yi ba matsala ba ne kowa da inda yake tashi, fargabar da na fara yi ita ce; saboda duk Kwana Casa’in ba magana nake yi ba, yawanci ina zaune ne, Farar Mace shi ma na yi maganganu amma maganganun sun bambanta da maganganun da na gani zan yi a Labarina, sai na fara tunanin zan iya ko ba zan iya ba. Gashi irin farkon zuwa na ne gurin, ban saba da su ba, bare na ce ko zan dan sake da su in dan cire kunya, saboda gaskiya ina da kunyar magana cikin mutane da yawa abun na ba ni wahala, to a haka har aka zo ‘shooting’ din haka in na karanta in aka zo aka dasa mun ‘camera’ sai na rika yi kamar ina karatu alamar dai ban kware da magana a fim ba. A haka dai tun ina yi, ina tsoro ina dari-dari har Allah ya taimake ni abun ya fara shiga jikina na fara yin ‘acting’ din yadda ya kamata. Amma idan masu kallo suka lura farko-farkon aktin dina ban saki jiki ba, akwai dan tsoro-tsoro akwai rashin fitar da magana yadda ya kamata, amma da abun ya fara shiga jikina muka saba da su sai na ga abun ashe ma ba komai ba ne kunya ce irin nawa amma idan ka dan cire kunyar nan a gefe to, za ka yi komai abin da na yi kenan, amma gaskiya na shiga wani yanayi a lokacin.
Lokacin da kika nuna wa iyayenki kina son shiga harkar fim, shin kin samu wani kalubale daga gare su ko kuwa?
Allah sarki, da na fara harkar fim.iyayena ba sa raye, ban da Uwa ban da Uba, Allah ya dauki abinsa. Sai ‘yan’uwana guda biyu sai familin babana da na mamana, gaskiya ban samu wani kalubalen a zo a gani ba har ga Allah. Saboda sun san wace ce ni kuma sun san abin da zan aikata, sun san abin da ba zan iya aikatawa ba. Kuma ba wai ina fariya ba ne ko ina koda kaina. Daidai gwargwado ina da nutsuwa, kuma ina da kamun kai, sun san ba zan taba zuwa na yi abin da zai zubar mun da mutunci ba har ya taba mutuncin gidanmu ba, sun san ba zan yi ba ina kokarin kiyayewa, duk da dai Dan’adam tara ya ke bai cika goma ba, amma ina kokarin kiyayewa. Ko da na zo na samu yayata na ce ina son na shiga harkar fim ba ta hanani ba iyakacinta dai nasiha na rike mutuncin kaina, in daraja kaina, in san kuma me nake, kuma kar na sake na yi abun da zai zubar mun da mutunci a cikin fim, shawarar da ta ba ni kenan, mutum daya ne ma na so na samu matsala da shi, shi ne Wana, shi ma kuma da yayata ta zauna na zauna na fahimtar da shi shikenan komai ya wuce.
Ya batun mutanen unguwa lokacin da a ka fara ganin fuskarki ta bayyana a fim, shin kin samu wani kalubale daga gare su ko kuwa?
Ma sha Allah, ban samu wani kalubale da mutanen unguwa ba, sai ma ‘Respect’ dina da ya karu a idonsu da yadda suke nuna mun suna son aktin dina abun ya yi musu dadi na kara burge su, tsakanina da su dai sai addu’a suke yi mun da faran alkhairi.
A iya shekarun da kika yi cikin masana’antar kannywood shin kin taba fuskantar wani kalubale daga cikin masana’antar?
Gaskiya ban taba fuskantar wani kalubale a cikin masana’antar Kannywood ba, ban taba samun ‘problem’ da kowa ba.
Wane irin nasarori ki ka samu game da harkar fim?
Gaskiya Alhamdu lillah duk da dai yanzu nake tashi yanzu ne duniya ta sanni, saboda koda na yi finafinai a baya ba wani sanina aka yi ba, in ban da sanadiyyar Labarina Allah ya daga ni, Labarina ya daga ni har aka sanni, to daidai gwargwado gaskiya ina samun nasarori, ba abin da zan cewa Allah sai godiya, kuma ina alfahari da shirin Labarina.
Da yawan masu kallo na ganin cewa Maryam ta yi miki girma matsayin ‘ya sai dai kanwa, shin ya kika ji a lokacin da a ka ce za ta fito matsayin ‘yarki?
Gaskiya da farko na ji wani iri zan fito a Uwa, kuma na kalli maryam zankadediyar budurwa, na kalli ‘ya’yana guda biyun nan, na ce “Anya zan kai a ce na haifi wannan ‘ya’yan?” sai na ce to fim ne kila akwai abubuwan da za su iya kara mun na fito a tsufan, saboda an kara mun, kuma aka nuna mun yadda zan rika manyancen saboda na fito a Uwar sosai. Amma da farko na ji wani iri sai na ga ni da ita kamar bambancin kadan ne, saboda a girme na girme ta, amma da na yi zabin ubangiji sai Allah ya yi mun wannan zabin sai na ji a jikina alkhairi ne na je na yi wannan rol din. Kuma da na fara ban ji komai ba sai na ji ina ma son rol din kuma da yadda mutane suka rika yabo na ana mun addu’o’i ana cewa mace tagari sai abun ya yi mun dadi, sai na ji dadin fitowa a Uwar, na ce yau da an ba ni rol din banza haka ‘yan kallo za su rika zagi na, mutuncina ya zube, amma an ba ni rol me mutunci kuma na ji dadi, na san fim ne ban kai shekarun da zan ajjiye wannan ‘ya’yan ba, kuma shi daman harkar fim za ka iya fitowa a tsohuwa, budurwa, yarinya, bazawara duk za ka iya fitowa ba wani abu bane, fim ne, amma yanzu ‘is normal’ ba komai wallah.
Kin taba samun wani kalubale game da haka?
Ban da fans da nake samun kalubale daga wajensu, kamar misali; Tiktok idan na hau ko na bi waka, sai ki ji ana cewa haba ke kuwa Uwa ce, Tsohuwa ce, Me zuciyar yara, me ka-za da ka-za, bai kamata kina haka ba mamanmu, saboda mutane kamar ba su da fahimta fim ne fa, wanda ma suka fi ni tsufa suka fi ni abu ma suna raye-raye a Tiktok bare ni da ba wani raye-raye nake yi ba, ta nan ne nake dan samun matsala da su, amma dai bai dame ni ba saboda ba kula su nake ba, gaskiya yanzu ina son rol din sosai.
Kamar ta bangaren masu neman aurenki, shin hakan ba ya shafarsu ta yadda za su rika ja baya ganin cewa ke ba yarinya ba ce kin yi musu tsufa, ko kin yi musu girma?Gaskiya ina samun wannan kalubalen, kuma abin da zai ba ki mamaki da yawa samari sun fi damuna a kan irin wannan abun, to ni daman ba ma’abociyar tara samari ba ce, ba ni da wannan ra’ayin, amma a ‘social media’ ina samun wasu ‘yan yara-yara za ki ga wani ma bai wuce irin 23 wani ma 25 zai rika maman Maryam ka-za-ka-za ‘seriously’, ina samun wannan ‘problem’ din, kuma yawancin wanda nake tare da su ai sun san ba tsohuwa ba ce, kawai aiki ne ya zo mun da haka, kuma dole na yi. Yawanci ma wasu in suka shiga Tiktok Profile dina sai ki ji ana cewa “Ashe ba tsohuwa ba ce”, wannan dai ban da matsala a kai.
Me za ki ce da masu yi miki irin hakan?
Kin san ba kyau wulakanta dan’adam kuma duk wanda ya ce yana son ka ba makiyinka ba ne masoyinka ne, to tsakanina da su sai dai na ce musu na gode-na gode, Allah ya bar so da kauna. Haka idan suka yi mun ‘comment’ wasu zan yi musu ‘Like’ wasu kuma na saka musu emoji dan murmushi, saboda babu kyau wulakanci mutum ya ce yana yi da kai ka wulakanta shi, wasu ina yi musu ‘comment’ wasu ba na yi musu, amma su sun san abin da ma ba zai yiwu ba ne kawai yaudarar kai ne, ina bin su ne a haka a rabu lafiya.
Wane waje kika fi so a cikin shirin Labarina, kuma wane waje ne ya fi ba ki wahala?
Eh! to, gaskiya dukka rol din da na yi ina son su kuma suna burge ni, dan ni ko ina kallo ina jin dadi, amma rol din da na fi so, shi ne rol din da a ka yi a asibiti wanda na mari Maryam, gaskiya ina matukar son rol din. Sannan kuma a tunanina ba rol din da ya ban wahala a cikin Labarina, idan ma akwai bai wuce wajen kuka ba dan yana bani wahala, ba komai ne ya ke saka ni kuka ba.
Mene ne ya burge ki a marin, shin an yi shi ne a gaske ko kuwa yadda aka tafiyar da shi ne ya ke burge ki, ya abin ya ke?
[Dariya] Ba na gaske ba ne, yadda aka bayar da aktin din ne da fada da tsawa, raina ya baci har na kai na mare ta, shi ne abin da ya burge ni, na ji dadin rol din asibitin nan.
Ya kika dauki fim a wajenki?
Abin da na dauki fim wa’anzantarwa, Nishadantarwa, da kuma sana’a. Na dauke shi matsayin sana’a kin san kowa da irin sana’ar da ta karbe shi, to ni gaskiya a nawa na dauki fim sana’a ce.
Ko kina da ubangida a cikin masana’antar Kannywood?
Gaskiya ba ni da ubangida a cikin masana’antar kannywood, ban san gaba ba ko zan yi, a yanzu dai babu.
Wacce irin tambaya mutane suke yawan yi miki?
Tambayar da suka fi yi mun ita ce; “Shekarunki nawa?” an fi yi mun tambayar.
Mene ne burinki na gaba game da fim?
Burina na gaba bai wuce Allah ya kawo miji na yi aure ba, tunda Allah ya cikan burina na shiga, kuma daidai iya gwargwado na samu abin da nake so.
Bayan harkar fim kina wata sana’ar ne?
Bayan fim ina ‘Business, ina saida kayan kamshin, turarukan wuta, da kuma su Abaya, zannuwa, takalma, dan ‘already” ina da shago.
Ya ki ke iya hada kasuwancinki da kuma harkar fim?
Batun hakan duk ba damuwa ba ne, saboda idan ba na nan ina da masu duba mun shago, inada ‘yar’uwa da take duba mun shago, kuma inada me aiki dana saka na hada su, ban da matsala a kan ‘Business’ dina, ina tafiyar da komai daidai yadda ya kamata.
Kafin ki fara fim wane jarumi ko jaruma ce take burge ki kuma me ya sa?
Kafin na fara fim cikin ‘ya fim da suke burge ni, Allah ya ji kansa da Rahma Ahmad S. Nuhu shi ya ke burge ni, saboda ba shi da girman kai kowa nashi ne. Dan ban taba mantawa mun taba haduwa da shi a Kaduna yadda ya karbe mu kamar irin ya san mu mun dade da shi, gaskiya a cikin ‘yan fim shi yake burge ni.
Wace shawara za ki baw a masu kokarin shiga harkar fim?
Shawarar da zan ba su; ba laifi ba ne dan sun shigo amma ita harkar fim yadda ka dauke ta haka za ta bi da kai, idan ka shigo kai ba me kamun kai bane haka za ta tafi da kai, idan ka shigo kai me ka mun kai ne, haka za ta tafi da kai. Shawarar da zan bayar idan za su shiga harkar fim su san hannun da za su fada, su san hannun da za su je kuma in suka je su yi kokarin ruke mutuncin kansu su rike darajarsu, kar su maida kansu kamar ba su san abin da suke yi ba, in an ce musu ka-za ne su ce to, in an ce su yi nan su ce to, in an ce su zauna nan su ce to, saboda suna son harkar fim, a’a! su yi kokari su ruke mutuncinsu su rike girmansu, su rike darajarsu, sai su ga ma an fi daukarsu da mahimmanci da daraja. Kuma ya zamanto yarinya in za ta shiga harkar fim ta yi kokari iyayenta su sani su ba ta goyon baya su amince to sai ta shiga harkar fim, shi ne za ta ga ci gaba a rayuwarta, kuma za ta ga yadda za su girmama ta su ba ta ‘respect’ saboda daga gidan iyayenta ta fito ta shiga harkar, kuma iyayenta sun sani, kuma da ta shigo ta yi kokarin rike mutuncin kanta, shawarar da zan ba su kenan kuma su sani daukaka ta Allah ce ba sai ka je ka yi wani abu ba shi ne za ka samu daukaka, a’a! In Allah ya sa da rabon ka za ka ci abinci a harkar za ka ci abinci a harkar ba sai ka je ka kauce hanya ba.
Me za ki ce da masoyanki masu ganin finafinanki?
Abin zan ce da su shi ne; ina godiya, Ubangiji Allah ya saka da alkhairi, Allah ya bar zumunci, Allah kuma ya kara dankon soyayya, Ubangiji Allah ya kara mana son Manzon Allah (S.a.w). Sannan shawarata da zan bawa masoya dan Allah idan sun ga mun yi wani abu na kuskure su rika fahimtar da mu suna kwatanta mana, ba wai su zage mu ba, ko aibanta mu, ko su fada mana wani magana da bai dace ba, dan Allah su rika fahimtar abu a kan fim ne wani ba halinshi bane kawai an sa shi ne yayi a fim, kuma na gode da kaunar da suke nuna min gida da waje na gode, Allah ya bar zumunci ya kara mana hakuri kuma ya kara muku hakuri, na gode ina yi musu fatan alkhairi har da makiyan ma nagode.
Ko kina da wadanda za ki gaisar?
Ina da wadanda zan gaisar, musamman ma Malam Aminu Saira, saboda ina alfahari da shi kuma ina godiya, sannan akwai yayana Uncle Yas shi ma ina godiya sosai, saboda yana kokari a kan rayuwata kuma yana taimaka mun daidai gwargwado, sannan ba zan manta da ‘yar’uwata ba mai suna Fatima wacce aka fi sani da Jummai ita ma ta ba ni kwarin guiwa kuma ta yi mun addu’o’i, sannan ba zan manta Ammalo ba na Kaduna ‘Camera Man’ ne shi ma ya taimaka gurin harkar fim dina sosai, saboda farko shi na fara yi wa magana har na shiga harkar, dan haka ina gaishe shi ina godiya Allah ya bar zumunci, Allah kuma ya kare mun su gabadaya, da musulmai gaba daya ina godiya wadannan ba zan taba mantawa da su ba.
Sannan a karshe ina gaida Dansudan shi ne ya fara yi mun fim din Farar Mace ina godiya, Ina gaida Yunusa Mu’azu wanda shi ya kira ni na zo wannan harkar bai manta da ni ba ina godiya sosai Allah ya bar zumunci, Allah ya saka da Alkhairi. Ina gaisar da Ali Camera Man, wanda ya ke mana camera mutumin arziki mutumin kirki, ina gaida Hussaini Sound, ina gaida Bafarawa, da Sadam, duk dai ana tare su ne masu aikin Labarina, ina gaida kowa da kowa da wanda bai ji sunanshi ba dan Allah ya yi hakuri, kuma ina gaida Director Ibrahim Bala, sannan kuma ina gaida ‘Yan Jaridar LEADERSHIP gaba daya musamman ma ke Rabi’at Sidi Bala ina gaishe ki sosai, Ubangiji Allah ya bar zumunci, Allah ya kara daukaka, Allah kuma ya ba da sa’a kan ayyukanki na gode sosai.