Shugaban jam’iyyar Socialist Party ta kasar Zambia, Fred M’membe, ya shaidawa wakilin CMG cewa, Shawarar Wayewar Kai ta Duniya (Global Civilization Initiative) da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar, wani nagartaccen tunani ne, wanda zai taimakawa dan Adam a kokarinsu na tabbatar da ci gaban duniya.
Mista M’membe ya fadi hakan ne a gefen taron “Demokuradiyya: Darajoji masu muhimmanci ga daukacin bil-Adama” wanda ya gudana a birnin Beijing na kasar Sin a kwanakin baya.
A cewarsa, cikin wannan Shawara da aka gabatar, an jaddada bukatar girmama dukkan kasashe, da sauraron ra’ayoyin dukkan bangarori, ba tare da lura da bambancin karfinsu ba. Wannan ra’ayi, ita ce hanya daya tilo da za a iya bi don tabbatar da zaman lafiya a duniya. Idan kuma an yi watsi da wannan hanya, tabbas za a samu rikici tsakanin kasashe da al’ummu daban daban. (Bello Wang)