Gwamnan jihar Filato Simon Lalong, ya nuna jin dadinsa bisa kokarin da ake yin a kawo karshen tashin hankali a karamar hukumar Bassa wadda fadace-fadace ya yi sanadiyyar kashe mutane masu yawa da asarar dukiya tsakanin manoma da makiyaya.
Gwamna Lalong wanda ya zama shaida kan wannan yarjejeniya tsakanin kabilar Irigwe da kuma Fulani da ke karamar hukumar Bassa ya ce, ya yi matukar farin ciki da wannan ci gaba da aka samu a wannan karamar hukuma, na kokarin samar da zaman lafiya da juna.
Saboda haka sai ya bukaci sauran yankunan jihar su dauki darasi daga wannan karamar hukuma. Sannan kuma ya bukaci dukkan al’ummar jihar su kasance masu tattalin zaman lafiya, da samar da ci gaba.
Gwamnan ya ce, tun loacin da ya zama gwamna a shekara ta 2015, ya zo ya tarar da rikicr-rikice tsakanin al’ummomi, wanda hakan ya zame masa babban kalubale a gwamnatinsa.
Kamar yadda ya ce, yanzu haka gwamnatinsa ta kara zage damtse wajen samun tabbataccen zaman lafiya a kowane lungu da sako da ke fadin jihar, saboda haka sai ya nemi hadin kai domin samun nasarar wannan manufa ta sa, ta tabbatar da zaman lafiya.