Kamfanin dab’i na kwamitin tsakiyar JKS, ya wallafa littafi mai kunshe da cikakkun bayanai da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya yi game da ayyukan da suka jibanci mata, da na gamayyar kungiyoyin mata da yara kanana.
Tun bayan taron wakilan jama’ar kasar Sin na JKS karo na 18 wanda ya gudana a shekarar 2012, kwamitin tsakiya na JKS mai shugaba Xi Jinping a matsayin jigo, ke kara dora muhimmanci ga ayyukan da suka shafi ci gaban mata, inda kwamitin ke ta kara azama a wannan fanni, kamar dai yadda wata sanarwa da kamfanin dab’in ya fitar a Lahadin nan ta bayyana.
Sanarwar ta kara da cewa, batutuwan da shugaba Xi ya tattauna a wannan fanni na da matukar muhimmanci, a bangaren ingiza nasarar ci gaban ayyukan mata a sabon zamani, da dorewar manyan manufofin kasa na daidaiton jinsi, da kare hakkoki, da moriyar mata da yara kanana bisa doka. (Mai fassarawa: Saminu Alhassan)