Tun bayan da kasar Sin ta kyautata matakan kawar da cutar COVID-19 a karshen shekarar bara, harkokin tattalin arziki da zamantakewa sun farfado cikin sauri, kuma al’ummun kasa da kasa na ta maraba da hakan, suna kuma fatan hakan zai ba da kwarin gwiwa ga tattalin arzikin duniya baki daya.
To sai dai kuma wasu kasashen dake son Sin ta sassauta matakan kawar da cutar COVID-19 a da, karkashin wakilcin Amurka, sun sanar da cewa za su dauki matakan kayyade shiga kasashensu ga masu yawon shakatawa na Sin bisa zargin cewa mai yiwuwa cutar COVID-19 daga kasar Sin ta haifar da sabon nau’in kwayar cutar.
Bisa ilmin kimiyya, kwayoyin cutar dake yaduwa yanzu a kasar Sin su ne BA.5.2 da BF.7, wadanda sun riga sun yadu a wurare daban daban na duniya a baya. Wannan na nufin cewa, yiwuwar bullowar sabbin nau’ikan kwayoyin cutar a sassa daban daban na duniya ta riga ta kasance. Don haka abun tambaya shi ne mene ne ma’anar hana shiga kasashen waje ga masu yawon shakatawa daga kasar Sin?
Tsakanin kasa da kasa, kasashen duniya dukkansu za su samu lokacin karbuwa yayin da suka canja matakan kawar da cutar COVID-19, don haka ba a bar Sin a baya ba.
Kaza lika, galiban kasashen duniya sun sassauta matakan kawar da cutar, amma me ya sa wasu kasashe suka dauki matakan hana shigar Sinawa su kadai? Cibiyar kula da cututtuka ta Turai ta nuna cewa, babu hujjar yin gwajin cutar COVID-19 ga masu yawon shakatawa na Sin.
A ra’ayin sisaya na wasu mutane na kasashen Turai da Amurka, ko Sin ta “sassauta” ko ta “tsaurara”, ba za ta yi daidai ba. Mummunan aikin siyasar su yana haifar da sabon yanayi na rabuwa da ta da rikici.
“Shekaru uku ke nan, Thailand ta yi ta jiranku har tsawon shekaru uku!” Hukumomin yawon shakatawa, da ofisoshin jakadancin kasashe daban daban dake Sin, sun gayyaci masu yawon shakatawa na Sin ta kafar Weibo da su tafi da kuma bude ido a kasashensu. Wannan ita ce babbar murya a cikin duniya. Aikin dakile cutar a fannin siyasa na wasu kasashe ba zai yi nasara ba, domin kuwa duniya na fatan a samu karin karfin hadin gwiwa tsakaninsu. (Safiyah Ma)