Duk da cewa, kasar Maldives ta shahara matuka tsakanin tsibiran yawon shakatawa a fadin duniya, amma al’ummun kasar sun taba damuwa saboda rashin gada da ta hada tsibiran kasar, ta yadda dole ne a bi ta jiragen ruwa, kuma idan an gamu da mummunan yanayi, sufuri na gamuwa da kalubale. Don haka al’ummun kasar suke da burin gina wata gada a kan teku, wadda za ta hada filin jirgin saman Male fadar mulkin kasar, da tsibiran dake kusa da birnin daga zuriya zuwa zuriya.
Bayan da shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya kai ziyarar aiki a Maldives a watan Satumban shekarar 2014, kasashen biyu sun tattauna kan batun gina wata babbar gada a kan teku, kuma sun nadawa gadar suna “Babbar gadar sada zumunta tsakanin kasar Sin da Maldives”.
Ya zuwa ranar 30 ga watan Agustan shekarar 2018, aka kammala gadar ketara teku ta farko a Maldives, wadda ta hada tsibirai uku na kasar. (Mai fassara: Jamila)