A watan Disamban shekarar 1978, an kira taro na 3 na kwamitin tsakiya na JKS na 11, bayan taron ne kuma aka fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga ketare a kasar Sin.
Sannu a hankali, kasar Sin ta kasance babbar kasa mafi saurin samun ci gaban tattalin arziki ta biyu a duniya, kuma ta cimma burin kubutar da miliyoyin al’ummarta daga kangin talauci. A yanzu haka ta kafa sabon tsarin wayewar kan bil Adam iri na zamanantarwa mai halayyar kasar Sin.
- Sin Ta Gina Cibiyoyin Fasahar Aikin Gona Na Gwaji Guda 24 A Afirka
- Xi Jinping Ya Aike Da Wasikar Taya Murnar Cika Shekaru 50 Da Kafuwar Kungiyar USCBC
Shin ko wadanne alherai manufar kasar Sin ta yin gyare-gyare, da bude kofa ga waje take haifarwa duniyarmu?
Bisa shawarar ziri daya da hanya daya da ta gabatar, kawo yanzu, kasar Sin ta riga ta daddale takardun hadin gwiwa da kasashe sama da 150, da kungiyoyin kasa da kasa fiye da 30, takardun da suka amfani al’ummomin kasashen da suka shiga shawarar.
Ana iya cewa, kasar Sin ta samu wata sabuwar hanyar zamanantarwa mai halayyar kasar Sin, da ta dace da yanayin da take ciki, bayan da ta aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje, kuma sakamakon da ta samu yana samar wa sauran kasashe masu tasowa abin koyi da sabon zabi, yayin da suke kokarin raya kasashensu.
A halin yanzu, ana fuskantar manyan sauye-sauye a fadin duniya, a karkashin irin wannan yanayi, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da sabon tunaninsa, na gina kyakkyawar makomar bil Adam ta bai daya, wanda ya nuna makomar ci gaban duniya a nan gaba, inda sau da yawa ya jaddada cewa, kasar Sin za ta kara bude kofa ga kasashen waje, kuma za ta kara habaka zamanantarwa mai halayyarta daga duk fannoni, bisa tushen samun ci gaba mai inganci, ta yadda za ta samar da sabbin damammakin hadin gwiwa ga sauran kasashen duniya. (Mai fassara: Jamila)