Don tabbatar da doka da oda, sakamakon murnan da ‘ya’yan jam’iyyar adawa ta NNPP suke yi kan nasarar da dan takararsu ya samu a zaben gwamnan jihar Kano da aka kammala, gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, dubban al’umar Kano ne suka fito kan tituna a safiyar yau Litinin domin murnar nasarar da dan takarar jam’iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida Gida ya samu.
- Da ɗumi-ɗuminsa: Abba Gida Gida Ya Lashe Zaɓen Gwamnan Kano
- An Sake Zabar Gwamna Sule A Matsayin Gwamnan Jihar Nasarawa A Karo Na 2
Sakamakon haka, kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar, Muhammad Garba ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar da safiyar Litinin.
Ya ce an yanke shawarar ne don hana ’yan daba su haifar da hargitsi a halin da ake ciki.
Kwamishinan ya yi kira ga jama’ar jihar da su kasance a cikin gida domin jami’an tsaro ba za su kyale kowa ko kungiyar da ke da niyyar haddasa fitina ba.
A halin yanzu Jami’an tsaro sun mamaye galibin titunan kuma an gan su suna korar wadanda suka bijirewa umarnin komawa gidajensu har zuwa lokacin da dokar ta-baci ta kare.