Saɓanin iƙirari da gwamnatin jihar Kano ta yi na cewa, jam’iyyar APC ce ta ɗauki nauyin zanga-zangar lalata dukiyoyin gwamnati a jihar a kwanakin baya, jam’iyyar ta zargi gwamnan jihar, Abba Yusuf, da daukar nauyin zanga-zangar don bata sunan gwamnatin da shugaba Bola Tinubu ke jagoranta.
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Ganduje ne ya yi wannan zargin a Abuja ranar Alhamis.
- Shari’a: Ganduje Ya Ki Na’am Da Tayin Jakadanci A Kasashen Afirka
- Ɗan Takarar Shugaban Ƙaramar Hukuma Zai Biya Naira Miliyan 10 A Kano
Wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren yada labarai na shugaban jam’iyyar APC na kasa, Edwin Olofu, ta ce, rahotannin sirri masu inganci sun nuna cewa, zanga-zangar da ta rikide zuwa hargitsi, gwamnatin Gwamna Yusuf ce ta dauki nauyinta a jihar Kano.
“Abin takaici ne yadda gwamna mai ci zai tada irin wannan rikici da tashin hankali a jiharsa, tare da jefa rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa da ba su ji ba ba su gani ba cikin firgici.
“Muna yin Allah-wadai da wannan hali na rashin da’a, wanda hakan wani yunkuri ne na kawo cikas ga zaman lafiya a Kano, da gurgunta zaman lafiya da tsaro a yankin, musamman don batawa Shugaban kasarmu suna.” In ji wani bangare na sanarwa