Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya zargi shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, da ƙara ta’azzara matsala ga al’ummar a jihar Kano, ta hanyar yin watsi da biyan sama da Naira biliyan 48 na haƙoƙin ‘yan fansho a tsawon shekaru takwas da ya yi yana mulki.
Da yake jawabi a wajen ƙaddamar da kaso na uku na biyan bashin Naira biliyan 5 na kuɗaɗen alawus-alawus ga waɗanda suka yi ritaya a ranar Alhamis, a gidan gwamnati Gwamna Yusuf, ya nuna matukar damuwarsa kan halin da ‘yan fanshon jihar ke ciki.
- Gwamna Yusuf Ya Gargaɗi Kwamishinoninsa Kan Duk Wani Yunƙurin Kawo Rarrabuwar Kai A Majalisar Zartarwar Kano
- Za a Fara Kera Motoci Da Babura Masu Amfani Da Lantarki A Kano
Gwamna Yusuf, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin-Tofa, ya fitar ya bayyana cewa jimillar kuɗaɗen tallafin da aka ware sun haura sama da Naira biliyan 48, lamarin da ya bayyana a matsayin babbar barazana ga zaman ci gaban da Kano, ta taba fuskanta tun bayan ƙirƙiro ta a shekarar 1967.
Gwamna Yusuf, ya bayyana cewa, domin rage raɗaɗin ’yan fanshon, gwamnatinsa ta raba Naira biliyan 16 ga ma’aikata 6,886 da suka yi ritaya, wanda hakan na daga cika alƙawarin da ya ɗauka lokacin yakin neman zabe na tallafa wa tsofaffin da suka yi wa jihar hidima, kana ya kuma umurci hukumar fansho na jihar da ta zakulo waɗanda suka rasa rayukansu domin biyan magadansu Naira miliyan 846 da ke adane.
Gwamna Yusuf ya kuma bayyana amincewa da ƙara mafi ƙarancin haƙƙin ‘yan fansho daga Naira 5,000 zuwa Naira 20,000 duba da yanayin rayuwa da hauhawar farashin kayayyaki da kuma tsadar rayuwa.