Kawo yanzu kasashe 20 ne suka samu gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai na Euro 22024 kai tsaye, wanda Kasar Jamus za ta karbi bakuncin wasannin a shekara mai zuwa ta 2024.
Kasar Ingila, wadda Gareth Southgate ke jan ragama tana cikin tawagogin da za su jira raba jadawali, bayan da ta ja ragamar rukuni na uku, itama Scotland ta samu gurbi na zuwa gasar.
- Shirin Rage Tsadar Rayuwa: Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Biyan Sabon Tsarin Albashi Daga Afrilun 2024 – Minista
- Masani: Zamanantarwa Irin Ta Sinawa Wani Sabon Salo Ne Na Wayewa
Dukkan wadda ta yi ta daya da ta biyu a kowanne rukuni, su ne suka samu tikiti kai tsaye a wasannin da za a fara daga watan Yuni zuwa Yulin na shekarar ta 2024 kamar yadda yake a doka.
Yanzu kenan saura gurbi uku ya rage, inda kasashe 12 za su buga wasannin cike gurbin shiga Euro 2024 domin samun kasashen da za su cike gurbin gasar da ake ganin za ta kayatar matuka.
Tawaga nawa ce za ta buga Euro 2024?
Kasa 23 ce za ta barje gumi a Euro 2024, inda Jamus da za ta karbi bakuncin wasannin ce kadai da ta samu takiti kai tsaye saboda a doka duk kasar da za ta karbi bakunci tana da tikiti kyauta.
A ranar Talatar watan da ya gabata aka kammala karawar cikin rukuni ta yadda aka samu kasashe 20 da suka kai Euro 2024 kai tsaye kuma su ne za su fafata tare da ragowar kasashe ukun da za su bi su nan gaba.
Kawo yanzu kasashen da suka samu gurbin shiga gasar sun hada da kasashen Sipaniya, Scotland, France, Netherlands, England, Italy, Turkey, Croatia, Albania, Jamhuriyar Czech, Belgium, Austria, Hungary, Serbia, Denmark, Slobenia, Romania, Switzerland, Portugal da kuma Slobakia.
Yanzu kasa uku za a tantance, bayan buga karawar cike gurbi, domin samun 24 da za su fafata a Jamus a 2024 kuma za a raba jadawalin cike gurbi bisa la’akari da kwazon tawaga a wasannin da suka buga a cikin rukuni.
Bayan raba jadawalin, kasar Wales za ta karbi bakuncin Filland a wasan cike gurbi na gasar Euro 2023 da Jamus za ta karbi bakunci sannan kasar da ta yi nasara cikinsu za ta buga wasan gaba da Poland ko Estonia a gida domin samun gurbi a gasar da za a fara a ranar 14 ga watan Yuni a kare a ranar 14 ga watan Yuli 2024.
A rukuni na biyu akwai wasa tsakanin Isra’ila da Iceland, yayin da Bosnia Herzogobina za ta karbi bakuncin Ukraine, sannan a rukuni na uku Georgia da Ludembourg ne za su fatata waca ta yi nasara kuma za ta barje gumi da Kazakhstan ko kuma Greece.
Yadda Aka Raba Jadawalin:
Rukunin (A) Poland da Estonia – Wales da Finland. Rukunin (B) Israel da Iceland.
Bosnia-Herzegobina da Ukraine. Rukunin (C) Georgia da Ludembourg Greece da Kazakhstan