A ranar Lahadi ne tawagar kwallon hannu ta maza ta Nijeriya ta lallasa takwararta ta kasar Kenya da ci 32-23 a wasansu na uku a gasar cin kofin kwallon hannu na maza da ake ci gaba da yi a kasar Masar.
Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya NAN ya ruwaito cewa wannan shi ne nasarar farko da tawagar ta samu bayan rashin nasara a wasanni biyu da suka buga da Angola da Tanzania.
NAN ta kuma ruwaito cewa yanzu Nijeriya za ta buga wasan neman gurbi da Jamhuriyar Congo a ranar Talata da karfe 7 na dare.
Golden Arrows kamar yada ake kiransu, sun kuduri aniyar samun nasara a wasannin gaba duk da cewar sunyi rashin nasara a wasanni biyu da suka buga a baya.