Assalamu alaikum masu karatu,
Barkan mu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata. Yau kuma za mu yi magana kan yadda uwargida za ta hada Gasasshen Nama mai Dankali.
Ga dai abubuwan da uwargida za ta tanada:
Nama, Dankali, Albasa, Tumatur, Kori, Magi, Mai:
Yadda za ki sarrafa:
Da fari za ki soya dankali ki kwashe ki ajiye a gefe, sannan ki yanka naman fale-fale kamar yankan dankalin, sai ki dora kasko a kan wuta ki zuba mai kadan idan ya yi zafi sai ki zuba naman nan a cikin kaskon ki zuba Magi da kayan kamshi, sai ki rage wutar ki rufe.
Bayan dan lokaci sai ki juya idan shi ma ya dan gasu ko ina, sannan ki zuba albasa da tumatur da attaruhu a kai, idan suka yi laushi sai ki dora dankalin a kan gasashshen naman ki rufe.
Bayan dan wani lokaci za ki ga duk kayan sun makale a jikin naman, shi kenan kin kammala.
A ci dadi lafiya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp