Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin dake Majalisar Dinkin Duniya, Dai Bing, ya bayyana a jiya Litinin cewa, kudi shi ne tushe kuma muhimmin jigo na harkokin majalisar, kuma gazawar wasu manyan kasashe na biyan kudin memba na dogon lokaci, shi ne babban dalilin da ya janyo karancin kudaden gudanarwa a majalisar.
A wajen bikin kaddamar da zaman kwamiti na biyar na babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 78, wato kwamitin kula da harkokin gudanarwa da kasafin kudi, jami’in ya bayyana cewa, daidaita wannan matsala na bukatar kokari daga fannoni daban-daban, kana, bai kamata a dauki mataki na wani gajeren lokaci ba.
A cewarsa, daidaita ayyukan MDD, na bukatar kokari a wasu manyan fannoni uku, wadanda ke kunshe da tsaro, da ci gaba da kuma hakkin dan Adam, da inganta hakkin sauraron ra’ayoyin kasashe masu tasowa game da harkokin MDD, da kara wakilcin kasashen a sakatariyar majalisar, a wani kokari na amsa damuwar kasashen da ba su da wakilci sosai ta hanyar daukar matakan zahiri, da taimakawa daidaita harkokin duniya ta hanya mafi dacewa da adalci. (Murtala Zhang)