Matashiya Gbemisola Yusuf mace ce mai hankoron jan ragamar rayuwarta da kanta domin tun tana shekara 21 da haihuwa ta fara alkalancin wasa a Nijeriya inda ta jagoranci wasanni 22 a filin wasa na Maracana da ke Legas.
Matakin da take kai a yanzu ba karamin abin alfahari ba ne saboda tana cikin alkalan wasa mata kalilan a Nijeriya duk da cewa an samu karuwar alkalan wasa mata a Afirka a ‘yan shekarun nan, har yanzu mata ba su da yawa a harkar alkalancin wasa a Afirka da duniya baki daya.
- Aikin Matatar Mai Na Ya Hana Ni Sayen Arsenal A 2020 – Dangote
- Ba Kare Bin Damo Tsakanin Man City Da Arsenal A Etihad
Zuwa shekara ta 2023, mata 53 ne kawai ke cikin alkalan wasa na hukumar kwallon kafa ta duniya, kuma sun kunshi mataimaka alkalin wasa, da alkalan wasan kwallon dabe (Futsal), amma hakan ma an samu karuwa duk da haka idan aka kwatanta da shekarun baya.
Afirka ta Kudu da Moroko ne suka fi yawan alkalan wasa mata da ke busa wasanni a babban mataki duk da cewa alkalan wasa mata kan fuskanci kalubale mai yawa a Nijeriya da Afirka saboda al’adu da addinai, sai dai da ma can al’adu kan hana mata shiga wasanni musamman ma kwallon kafa.
Gbemisola Yusuf, wadda aka haifa a yankin Agege na Jihar Legas, filin wasan da ke yankin muhimmin abu ne a rayuwarta da ma danginta domin lokacin da take yarinya, takan je filin wasan tare da mahaifiyarta suna sayar da ruwa da lemo ga ‘yanwasa, da masu koyarwa, da ma ‘yankallo kuma a wannan lokacin ne sha’awar kwallon kafa ta shiga rayuwarta.
Bayan ta fara a matsayin ‘yar wasa, Gbemisola ta koma akalancin wasa domin wani mai gidanta mai suna Dele Atoun, tsohon alkalin wasa kuma sakataren majalisar alkalan wasa ta Legas, kan tuna lokacin da ta fara wasa.
Ya ce ta gina kwarin gwiwa a ranta duk da yadda take ganin ana kai wa alkalan wasa hari, ana jifan su, amma kuma ta ga yadda suka yi nasara kuma hakan ya kara wa mata kwarin gwiwa domin nan gaba ma wasu su fito.
Gbemisola ta fara alkalancin wasa lokacin da take shekara 14 da haihuwa bayan ta shiga wani shiri da hukumar kwallon kafar Afirka CAFN ta shirya domin zakulowa da kuma ba da horo ga matasa a alkalancin wasa.
Sai dai hanyar da ta bi ba mai sauki ba ce musamman a Nijeriya, saboda cin zarafi ta hanyar kalamai da ma yadda magoya baya kan kai wa alkalan wasa da ‘yanwasan hari amma duk da haka ta jure har ta cika burinta.
Wani bincike da kungiyar alkalan wasa ta Nijeriya NRA ta gudanar ya nuna cewa kashi 80 cikin 100 na mutanen da suka ba da amsa sun ce sun fuskanci wani nau’i na cin zarafi a lokacin da suke alkalancin wasa.
Itama Gbemisola ta fuskanci irin wannan yanayin amma kuma hakan bai sanyaya mata gwiwa ba inda ta ce alkalancin wasa ne aiki mafi wahala a duniya domin za ka yanke hukunci a cikin ‘yan dakikoki, ko da kuwa ka yi daidai ko akasin haka. Muhimmiyar damar da Gbemisola ta samu ita ce, lokacin wani wasa a Legas tana ‘yar shekara 18. Alkalan wasan ba su zo ba, ‘yan mintuna kafin lokacin take wasan, sai aka nemi Gbemisola da ke taimaka wa mahaifiyarta sayar da ruwa a filin wasan ta jagoranci wasan kuma kusan ta yi komai daidai a wasan, kuma hakan ya ja hankalin mutane da yawa.
Daga nan ne kuma Gbemisola ta daukaka, inda har ta yi busa a gasar Firimiyar Nijeriya ta mata amma kuma kai wa wannan mataki ma na da nasa kalubalen, musamman ga mata domin hari kan alkalan wasa a Nijeriya ba sabon abu ba ne, kuma ya kan hada da zagi da ma kai hari.
A 2021, wasu ‘yankallo sun kori wata alkaliyar wasa yayin wani wasan hamayya, lamarin da ya jawo tir daga hukumar kwallon kafa ta Nijeriya da kuma kiraye-kirayen tsaurara tsaro yayin wasanni musamman kan mata alkalan wasa.
Tun daga 2023, babu wata gasa a Nijeriya da ta fara amfani da na’urar BAR mai taimaka wa alkalin wasa, kuma hakan ya sa alkalan wasan Nijeriya ba su iya busa wasanni a wasannin duniya saboda ba su iya amfani da na’urar ba.
Gbemisola ta ce idan har ta dage da kokari a aikinta, ba ta da wata fargaba domin kuwa ta kan yi bakin kokarinta kawai ta bar wa Allah sauran domin a alkalancin wasa ba komai za ka yi daidai ba kuma ba zaka taba farantawa kowa rai ba.
A rayuwar Gbemisola, filin wasa na Agege ba wuri ba ne kawai, wata alama ce ta mafarin sana’arta domin duk da cewa yanzu ta daina sayar da ruwa saboda Jami’ar Legas da take zuwa karatu, ba ta manta da wannan lokaci ba.
“Komai na rayuwata ya ta’allaka ne da filin wasa na Agege domin a nan na samu kwarin gwiwar shiga aikin alkalancin wasa, kuma yankin gaba dayansa ya taimaka min sosai.”
A lokacin da take hira da manema labarai.
Gbemisola na cikin alkalan wasan da suka busa gasar makarantu ta Afirka, inda ta shiga wasannin neman gurbi da kuma gasar kanta a Tanzania domin a cewarta, burinta ne ya cika kuma ta ji dadin yin hakan, kamar yadda ta bayyana.
Ta ci gaba da cewa “Zuwa kasashe da kuma tattaunawa da alkalai daban-daban, da kuma koyon harsuna abubuwa ne da suka taimaka mata domin iya magana da harsuna daban-daban kan taimaka wa alkalin wasa wajen karfafa ikonsa a cikin fili.
Ta kara da cewa abu ne mai muhimmanci sosai saboda ba ta taba tsammanin za ta hadu da mutanen da ta gani ba kuma shi ma mai gidanta Atou ya ce yana alfahari da nasarorinta domin labarinta mai karfafa gwiwa ne da jajircewa.