A safiyar yau Talata ne ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya shirya taron watsa labarai, inda aka yi bayani kan yanayin gudanarwar tattalin arzikin kasar a rubu’in farko na shekarar bana ta 2023.
Jami’in hukumar kididdigar kasar ya yi tsokaci da cewa, sakamakon kididdigar da aka samu bisa mataki na farko ya nuna cewa, adadin GDP na kasar a rubu’in farkon bana ya kai kudin Sin yuan biliyan 28499.7, adadin da ya karu da kaso 4.5 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara, kuma ya karu da kaso 2.2 bisa dari idan aka kwatanta da rubu’in karshe na bara. Daga cikinsu, adadin dake shafar kayayyakin aikin gona ya karu da yuan biliyan 1157.5, wato ya karu da kaso 3.7 bisa dari kan na makamancin lokaci a bara.
- Kasar Sin Ta Soki Amurka Bisa Kakabawa Wasu Kamfanoninta Takunkumi Dangane Da Batun Maganin Fentanyl
Kaza lika adadin dake shafar kayayyakin masana’antu ya karu da yuan biliyan 10794.7, adadin da ya karu da kaso 3.3 bisa dari. Sai kuma adadin dake shafar sana’o’in samar da hidima wanda ya karu da yuan biliyan 16547.5, adadin da ya karu da kaso 5.4 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin lokaci a bara.
A takaice dai ana iya cewa, tattalin arzikin kasar Sin ya gudana yadda ya kamata a rubu’in farko na bana, sakamakon kyautatuwar yanayin kandagarkin cutar COVID-19, da aiwatar da matakan sa kaimi kan karuwar tattalin arziki, da tabbatar da samun guraben aikin yi da daidaiton farashin kayayyakin da gwamnatin kasar ta dauka. (Mai fassarawa: Jamila)