Hukumar lura da kayayyakin gadon al’adun gargajiya ta kasar Sin, ta ce a shekarar 2023, gidajen adana kayan tarihi na kasar sun karbi baki masu ziyara da yawansu ya kai biliyan 1.29, adadin da ya dara na shekarar 2022.
Hukumar ta bayyana alkaluman ne a Asabar din nan, yayin bikin ranar gidajen adana kayan tarihi ta kasa da kasa da aka gudanar a birnin Xi’an, babban birnin lardin Shaanxi na arewa maso yammacin kasar Sin.
- Amurka Za Ta Lashe Amanta Game Da Karin Harajin Rashin Adalci Da Ta Bugawa Kasar Sin
- Ribar Gajiyar Masana’antun Ba Da Hidimar Tauraron Dan Adam Na Ba Da Jagorancin Taswira Na Sin Ta Karu Da 7% A Bara
A cewar hukumar, a shekarar ta bara, gidajen adana kayan tarihi dake sassan kasar Sin sun gudanar da nune-nune sama da 40,000, da ayyukan ilmantarwa sama da 380,000.
Har ila yau a dai shekarar ta 2023, an yi rajistar sabbin irin wadannan gidaje har 268 a sassan kasar Sin, wanda hakan ya kai jimillarsu zuwa 6,833. A daya bangaren kuma, kasar Sin na kara fadada aiwatar da manufar baiwa al’umma damar ziyartar gidajen adana kayan tarihin kyauta, inda kawo yanzu sama da kaso 90 bisa dari na gidajen ana ziyartar su ne kyauta. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp