Gidauniyar Bafarawa ta tallafa wa yara masu zanga-zangar tsadar rayuwa wadanda aka kama a kwanan baya da tallafin kudi naira miliyan 18 a matsayin jari da za su fara sana’o’in dogaro da kai.
Yaran wadanda aka saki a makwan da ya gabata su 119, sun samu tallafin naira dubu hamsin- hamsin kowannensu.
- Sin Ta Kafa Tsarin Ilimin Koyar Da Sana’o’i Mafi Girma A Duniya
- Ya Kamata Rungumar Hadin Gwiwa Da Yin Komai A Bude Su Zamo Ginshikan Ci Gaban Yankin Asiya Da Pacifik A Nan Gaba
Taron raba musu jarin ya gudana a gidan tunawa da Sardauna da ke Jihar Kaduna karkashin jagirancin Dakta Suleiman Shinkafi da Malam Abdulrahman Baffa Yola.
Gidauniyar Bafarawa ta bayyana matakin a matsayin tallafa wa yaran da aka kama yayin gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwwa wadanda daga bisani aka sako su.
Gidauniyar ta ce ya zama wajibi su taimaka wa matasan da jari domin fara gudanar da sana’o’i da za su dogara da kansu maimakon kara shiga wata zanga-zangar nan gaba.
Dakta Shinkafi Bafarawa ya yi amfani da bikin mika kudaden wajen jawo hankalin matasan da su kaucewa shiga duk wani shiri domin ta da zaune tsaye. Yana mai cewa gidauniyar Bafarawa ta tallafa wa matasan da kudi naira dubu 50 kowannensu wanda a jimmala ce aka ba su naira miliyan 18.
Jihar Kaduna na daya daga cikin jihohin arewa da aka kama yara masu zanga-zangar, wanda aka kama sama da yara 30.