Babu shakka tsarin cinikayya tsakanin kasashen duniya na cikin mawuyacin hali, amma ziyarar aiki ta shugaban kasar Sin Xi Jinping a kasashen Vietnam, Malaysia da Cambodia wacce ta kasance ziyararsa ta farko a kasashen waje a bana, ta sanya wani sabon kuzari da ci gaba tare da ingiza fata a yankin kudu maso gabashin Asiya da ma duniya baki daya.
Vietnam, a matsayinta na makwabciyar gurguzu dake samun ci gaba da yin gyare-gyare bisa ga yanayinta na kasa, ta kasance zangon farko na rangadin kwanaki biyar da Xi ya yi a kudu maso gabashin Asiya. A shekarar 2023, Sin da Vietnam sun amince su gina wata al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya, kuma mai matukar mahimmanci bisa tushen zurfafa hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare. Yayin da kasashen biyu suka rattaba hannu kan takardun hadin gwiwa guda 45 a yayin ziyarar Xi ta wannan karo, wadanda suka hada da inganta cudanya da juna, da binciken kwastam da ayyukan da suka shafi kebence hajoji, da cinikayya a fannin noma, da al’adu, da fasahar kere-kere da dai sauransu. Wannan huldar za ta haifar da ci gaban zamantakewa a tsakanin kasashen biyu.
- Tsakanin Kafa Shingaye Da Gina Gada: Yadda Matakan Amurka Da Sin Suka Bambanta Sosai
- Tawagar Gwamnati Ta Kai Ziyara Filato, Ta Sha Alwashin Kawo Karshen Kashe-kashe A Jihar
Kazalika, ziyarar ta Xi a Malaysia ta wannan karo ta zo ne bayan ziyararsa ta farko a kasar yau shekaru 12 da suka gabata, wadda ta zama wata muhimmiyar ci gaba a dangantakar dake tsakanin Sin da Malaysia. Bugu da kari, Xi ya gabatar da shawarwari mai kunshe da abubuwa uku kan gina al’ummar Sin da Malaysia mai kyakkyawar makomar bai daya bisa manyan tsare-tsare. Idan ba mu manta ba, Malaysia na daga cikin kasashen farko da suka shiga hadin gwiwar shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya”. A yayin ziyarar ta Xi, kasashen biyu sun sake jaddada aniyarsu ta karfafa hadin gwiwa a karkashin shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya”, inda hadin gwiwar Beijing da Kuala Lumpur ta samu ci gaba cikin ‘yan shekarun da suka gabata.
Kasar Cambodiya ce zangon ziyararsa ta karshe. Inda kasashen biyu suka amince da gina al’umma kyakkyawar makomar bai daya a sabon zamani, wanda kamar yadda bangarorin biyu suka jaddada, ya dace da muhimman muradun jama’ar kasashen biyu. La’akari da kalubalan da ake fuskanta a tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban daban, kasar Sin ta taka rawa wajen samar da zaman lafiya a duniya. Kuma ziyarar shugaba Xi a kudu maso gabashin Asiya a daidai lokacin da duniya ke fuskantar barazanar bangaranci da daukar matakai bisa radin kai da Amurka ta rike a matsayin makamin mu’amalantar sauran kasashen duniya, ta sa kaimi ga samar da zaman lafiya da wadata a yankin da ma duniya baki daya. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp