Sabon rahoton da cibiyar tattara bayanan intanet ta kasar Sin wato CNNIC ta fidda ya nuna cewa, a halin yanzu, yawan mutanen dake amfani da fasahar kirkirarriyar basira ta AI ta salon koyo da kai don samar da bayanai wato Generative Artificial Intelligence a kasar Sin ya riga ya zarce miliyan dari 5, hakan ya ba sana’o’i daban daban a cikin kasar kwarin gwiwar kyautata ayyukansu da fasahar AI, da kuma samar da sabon karfi ga aikin gina kasar Sin ta dijital.
A tsakanin shekarar 2021 zuwa shekarar 2025, wato lokacin da Sin ta aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar biyar karo na 14, kasar ta cimma gaggaruman nasarori a fannonin raya harkokin dijital, da intanet, da fasahar AI. A halin yanzu, kasar Sin ta kasance gaba a fannin yawan gina ababen more rayuwa da ma fasahohin da suka shafi harkokin dijital, inda ta cimma nasarar gina dandalin koyarwa da fasahar kirkirarriyar basira ta AI, wanda ya fi samun albarkatu, da nau’o’in bayanai, da masu amfani da shi, kuma mafi girma a duk fadin duniya, lamarin da ya sa fasahar AI ke tallafawa al’umma.
A sa’i daya kuma, an kyautata fasahar AI a dukkanin fannoni bisa tsari, kana yawan lambobin kira da kasar Sin take da su a fannin fasahar AI ya kai kaso 60 bisa dari na duk fadin duniya, hakan ya sa, kasar Sin ta zama daya daga cikin cibiyoyin kirkire-kirkiren fasahar AI na duniya. Kyautatuwar fasahar AI da fasahohin sadarwa sun gaggauta ginuwar masana’antu masu aiki da fasahar AI cikin kasar, wadanda suka shafi kaso 80 bisa dari na sana’o’in kere-kere, lamarin da ya ba da gudummawa ga bunkasuwar ayyuka masu inganci. (Mai Fassara: Maryam Yang)