• English
  • Business News
Wednesday, October 29, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gina Mutane Don Bunkasa Hazakarsu Na Daga Cikin Ajendar Sin Na 2025

by CGTN Hausa and Sulaiman
8 months ago
Sin

LABARAI MASU NASABA

An Samu Ingantuwar Yanayin Iska Da Ruwa Cikin Watanni 9 Na Farkon Bana A Sin

Yadda Kasar Sin Ke Kara Kyautata Tsarin Kare Muradun Al’umma A Bangaren Shari’a

Kirkira ita ce kashin bayan ci gaba, kuma hazaka ita ce ginshikin kirkira. A zamanin yau, fannoni masu tasowa musamman na fasahar zamani kamar kirkirarriyar basira (AI) da sauransu suna bunkasa, kuma akwai bukatu na matukar gaggawa ga sabbin hazaka. Hakan ya sanya kasar Sin ta maida hankali kan raya hazaka tun wuri-wuri, da kara zuba jari a fannin ilimi, da dasa iri na kirkire-kirkire don ya tsira a cikin zukatan matasa ta hanyar “zuba jari kan gina mutane”. Matakan da aka ambata a cikin rahoton aikin gwamnati a taruka biyu na bana, kamar bayar da tallafin tarbiyyar yara da karfafa tsare-tsaren tabbatar da kowane yaro ya samu ilimi ala tilas, ayyuka ne masu haske ga wannan manufa ta “zuba jari kan gina mutane” a fagen ilimi. Wannan manufa ba wai kawai ta mayar da hankali kan daidaikun mutane ba ne, har ma da la’akari mai zurfi ga ci gaban al’umma gaba daya. Manufar tana kuma mayar da hankali ga dukkan tsarin rayuwa la’akari da yanayi mai sarkakiya da muke ciki. Hakazalika, tsarin daidaitawa da fadada ayyukan yi na ba da cikakkiyar damar nuna hazakar mutane da kuma fahimtar kimarsu, kamar dai yadda tsarin bunkasa yawan kudin shiga na mazauna ke iya habaka tunaninsu game da hanyoyin samun riba da karin farin ciki da kwanciyar hankali.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron tattaunawa da nazari kan ganawar da wakilan jam’iyyar CPPCC daga fannonin kimiyya, fasaha da ilimi, wanda ya fitar da kwakkwaran matakai game da hangen nesa a ranar 6 ga watan nan da muke ciki, wanda ya jaddada muhimmancin kimiyya da fasaha da ilimi da hazaka ga zamanantar da kasar Sin, inda shugaba Xi ya jaddada cewa a nan gaba, ya kamata kasar Sin ta rungumi wani yanayi mai haske, inda za a samu masu kwazo da hazaka masu dimbin yawa, ta yadda kowa da kowa zai baje kolin basirarsa kuma a yi amfani da su yadda ya kamata. Har ila yau, a cikin rahoton aikin gwamnati na bana, an gabatar da sabbin dabarun “zuba jari kan gina mutane” a karon farko, wanda kamar fitila, ya haskaka muhimmin alkibla ga ci gaban kasar Sin a nan gaba. Sanin kowa ne cewa, a cikin ’yan shekarun nan, gwamnatin kasar Sin a dukkan matakai ta samu sakamako mai ban mamaki a fannonin zuba jari na zahiri wadanda suka shafi ababen more rayuwa, da kawo sabbin salon gudanar da harkokin birane da kauyuka. (Mohammed Yahaya)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Samu Ingantuwar Yanayin Iska Da Ruwa Cikin Watanni 9 Na Farkon Bana A Sin
Daga Birnin Sin

An Samu Ingantuwar Yanayin Iska Da Ruwa Cikin Watanni 9 Na Farkon Bana A Sin

October 29, 2025
Yadda Kasar Sin Ke Kara Kyautata Tsarin Kare Muradun Al’umma A Bangaren Shari’a
Daga Birnin Sin

Yadda Kasar Sin Ke Kara Kyautata Tsarin Kare Muradun Al’umma A Bangaren Shari’a

October 29, 2025
Binciken ‘Yan Sanda Kan Wanda Ake Zargi Da Tawayen “‘Yancin Kan Taiwan” Mataki Ne Na Adalci Don Kare Hadin Kan Kasa
Daga Birnin Sin

Binciken ‘Yan Sanda Kan Wanda Ake Zargi Da Tawayen “‘Yancin Kan Taiwan” Mataki Ne Na Adalci Don Kare Hadin Kan Kasa

October 29, 2025
Next Post
Kasancewar “Taiwan A Matsayin Lardin Kasar Sin” Shi Ne Matsayin MDD A Ko Yaushe 

Kasancewar “Taiwan A Matsayin Lardin Kasar Sin” Shi Ne Matsayin MDD A Ko Yaushe 

LABARAI MASU NASABA

majalisar kasa

Majalisar Wakilai Ta Amince Da Bukatar Amso Bashin Dala Biliyan 2.34 A Kasuwar Jari Ta Duniya

October 29, 2025
An Samu Ingantuwar Yanayin Iska Da Ruwa Cikin Watanni 9 Na Farkon Bana A Sin

An Samu Ingantuwar Yanayin Iska Da Ruwa Cikin Watanni 9 Na Farkon Bana A Sin

October 29, 2025
Kotu Ta Umarci Ƙwace Dala 49,700 Daga Tsohon Jami’in INEC

Kotu Ta Umarci Ƙwace Dala 49,700 Daga Tsohon Jami’in INEC

October 29, 2025
Yadda Kasar Sin Ke Kara Kyautata Tsarin Kare Muradun Al’umma A Bangaren Shari’a

Yadda Kasar Sin Ke Kara Kyautata Tsarin Kare Muradun Al’umma A Bangaren Shari’a

October 29, 2025
COAS Shaibu Ya Sha Alwashin Murƙushe ‘Yan Ta’addar Lakurawa 

COAS Shaibu Ya Sha Alwashin Murƙushe ‘Yan Ta’addar Lakurawa 

October 29, 2025
Binciken ‘Yan Sanda Kan Wanda Ake Zargi Da Tawayen “‘Yancin Kan Taiwan” Mataki Ne Na Adalci Don Kare Hadin Kan Kasa

Binciken ‘Yan Sanda Kan Wanda Ake Zargi Da Tawayen “‘Yancin Kan Taiwan” Mataki Ne Na Adalci Don Kare Hadin Kan Kasa

October 29, 2025
Afuwar Tinubu Ga Fursunoni: Saura Ƙasa Da Shekaru 6 Maryam Sanda Ta Shaƙi Iskar ‘Yanci

Afuwar Tinubu Ga Fursunoni: Saura Ƙasa Da Shekaru 6 Maryam Sanda Ta Shaƙi Iskar ‘Yanci

October 29, 2025
Xi Jinping Zai Gana Da Donald Trump

Xi Jinping Zai Gana Da Donald Trump

October 29, 2025
Gwamnatin Rikon Kwarya: Shirin DSS Ne Na Damke Atiku Da Peter Obi Kafin Rantsar Da Tinubu

DSS Ta Kama Wani Matashi Da Ya Yi Kira A Yi Juyin Mulki A Kafofin Sada Zumunta

October 29, 2025
An Kashe Ɗan Sanda Da Ɗan Hakimi A Rikicin Manoma Da Makiyaya A Gombe

An Kashe Ɗan Sanda Da Ɗan Hakimi A Rikicin Manoma Da Makiyaya A Gombe

October 29, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.