Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya kaddamar da aikin gina hanyar Wamba-Waiye-Dengi-Alizaga mai tsawon kilomita 24.5 a Kananan Hukumomin Wamba da Akwanga.
An ba da kwangilar aikin ne ga kamfanin Centerfield Engineering Limited a kan kudi naira biliyan 9,061,627,000.00, kuma ana sa ran hanyar za ta kasance wata muhimmiyar hanya ta bunkasa tattalin arzikin jihar, wadda za ta haɗa al’ummomi tare da bunkasa harkokin noma, kasuwanci da sauƙaƙa zirga-zirga.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Da Dama A Kauyukan Zamfara
- Amurka Ta Gargaɗi Ƴan Nijeriya Kan Zuwa Ƙasarta Domin Haihuwa
A cikin jawabinsa, Gwamna Sule ya jaddada muhimmancin gina titunan karkara, yana mai cewa, hakan na bai wa manoma damar jigilar kayan amfanin gona da sauran kayayyakin kasuwanci daga kauyuka zuwa birane. Ya kara da cewa, gina tituna a karkara yana da mahimmanci fiye da wasu tituna a birane. Saboda gina titi a karkara yana mayar da yankunan su zama maraya, inda al’umma za su yi ta suna zirga-zirga gudanar da harkokin kasuwanci dake kawo saukin abinci.
Gwamnan ya bukaci kamfanin da ke aikin da ya bi ka’idoji da tsarin tsaro, tare da roƙon al’ummomin da abin ya shafa da su ba da haɗin kai ga masu aikin da kuma kare rayuka da kayan aiki.
“Wannan aiki wani ɓangare ne na kudirin Gwamnatin Jihar wajen samar da ci gaban ababen more rayuwa domin bunkasa tattalin arziki da tabbatar da ganin cigaba ya kai kowane yanki,” in ji Gwamna.
Da yake kaddamar da aikin, Gwamna Sule ya sake jaddada kudirin Gwamnatinsa na kada a bar ko wata al’umma a baya wajen kawo ci gaba, domin samar da jihar Nasarawa da tabbatar da lafiya da haɗin kan ‘yan jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp