Wani gini a Babban Birnin Tarayya, Abuja, ya rufta da mutane da dama da ke a yankin Gwarinmpa.
Ginin wanda ya rufta a safiyar yau Alhamis, wata majiya ta ce, an ciro gawarwakin wasu mutunen da suka mutu.
- CBN Da ‘Yansanda Za Su Sa Kafar Wando Daya Da Masu Sayar Da Sabbin
- Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Aike Da Murja Kunya Zuwa Gidan Yari
Darakta a Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Abuja (FEMA), Florence Wenegieme, ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta ce, an kubutar da mutane 11 an kuma kai su babban asibitin Gwarimpa don duba lafiyarsu.
Florence, ta kara da cewa, jami’an hukumar na ci gaba da kokarin kubutar da sauran mutanen da lamarin ya rutsa da su.
A watan Agustan 2022 wani bene mai hawa biyu a anguwar Kubwa ya rufta, inda mutum daya ya mutu wasu kuma suka jikkata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp