A ‘yan kwanakin nan ne al’uimmar duniya suka tashi da wata mummunan girgizar kasar da aka dade ba a ga irinta ba a kasar Moroko inda zuwa yanzu aka tabbatar da mutuwar mutum fiye da 3,000, duk da wasu da dama na kwance a asibitoci ana kuma ci gaba da zakulo mutanen da suka makale a baraguzan gine-ginen da suka dannesu.
Wani abin al’ajabi a na kuma shi ne yadda al’umma duniya suka hadu wajen jajatanwa tare da kai agajin gaggwa don tallafa wa wadanda suka jikkata da kuma bayar da taimakon gaggawa ga wadanda suka tsira.
Gidan talbijin na Moroko, wanda ya ambato ma’aikatar harkokin cikin gida ta kasar tana bayyana haka, ya kara da cewa a kididdigkr fkro mutum 672 ne suka jikkata sakamakon girgizar kasar mai karfin maki 7.0 da ta kassara yankuna da dama na kasar.
Girigizar kasar ta kuma lalata gine-gine yayin da mutane suka rika tserewa daga gidajensu cikin firgici.
“Rahoton wucin-gadi ya nuna cewa girgizar kasar ta kashe fiye da mutum 3000 a larduna da biranen al-Haouz, Marrakesh, Ouarzazate, Azilal, Chichaoua da kuma Taroudant,” in ji sanarwar, wadda ta kara da cewa an garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibiti.
Wasu bidiyoyi da aka rika watsawa a shafukan sada zumunta wadanda ba a tantance sahihancinsu ba sun nuna yadda gine-gine suka rika rushewa yayin da wasu suke girgiza. An ga mutane cikin dimuwa yayin da wasu suke fitowa daga baraguzan gine-gine.
“Mun ji wata mahaukaciyar girgiza. Daga nan na fahimci cewa girgizar kasa ce. Mutane sun fada cikin firgici da yamutsi. Yara suna ta kuka yayin da iyaye suka dimauce,” kamar yadda Abdelhak El Amrani, wani mazaunin Marrakesh ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP ta wayar tarho.
Hukumar da ke nazari kan girgizar kasa ta Amurka [USGS] ta ce bayanan farko sun nuna cewa girgizar kasar da ta auku a Maroko tana da karfin maki 6.8 kuma ta faru a nisan kilomita 18 daga karkashin kasa.
Ta ce girgizar kasar ta faru ne da misalin karfe 11:11 na dare a agogon kasar kuma ta fi kamari a yanki mai fadin kilomita 56.3 a yammacin Oukaimeden, fitaccen wurin yin wasan zamiya da ke Tsaunukan Atlas.
Kafofin watsa labaran Maroko sun ce girgizar kasar ita ce mafi karfi da kasar ta taba fuskanta a tarihinta.
An ji karar girgizar kasar a Algeria da ke makwabtaka da Maroko, ko da yake Jami’an Tsaron Algeria sun ce ba ta yi wata barna ba.
A 2004, akalla mutum 628 ne suka mutu yayin da 926 suka jikkata sakamakon girgizar kasar da ta auku a Al Hoceima da ke arewacin Maroko.
Zuwa yanzu ana ci gaba da bayar da agaji kayan abinci da magunguna don, ana kuma ci gaba da zakulo wasu daga cikin baraguzan gine-ginen.
Ana cikin wannan alhinin ne kuma labarin wata mummuna ambaliyar ruwa da guguwar da ta ratsa kasar Libiya ta ruiski al’umma duniya, inda ita ma zua yanzu aka yi asarar rayukar mutane da duniyoyi na biliyoyn daloli.
Shugabannin duniya sun mika sakon jaje ga al’umma kasar, cikin na gaba-gaba a mika sakon jajen shi ne shugaban kasa Sin Di Jinping ya mika sakon jejen ga Mohamed Menfi, shugaban majalisar gudanarwar Libya, dangane da mahaukaciyar guguwar da ta afkawa kasar Libya.
A cikin sakon nasa, shugaba Di ya ce, ya kadu matuka da samun labarin mahaukaciyar guguwar da ta afkawa kasar, lamarin da ya janyo hasarar rayuka da dukiyoyi.
A madadin gwamnati da al’ummar Sinawa, Di ya yi jimami matuka ga wadanda abin ya shafa, tare da nuna jaje ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu da ma wadanda suka jikkata. Haka kuma shugaba Di ya bayyana imaninsa cewa, ko shakka babu al’ummar Libya za su shawo kan illar iftila’in.
Ma’aikatar lafiya ta Libiya ta bayyana yau cewa, akalla mutane fiye da 5, 000 ne suka mutu yayin da sama da dubu biyar suka bace a birnin Derna na kasar, bayan da wata mummunar ambaliyar ruwa da ta mamaye gabashin kasar a ranar Lahadin da ta gabata.
Haka kuma a halin yanzu kasashen duniya na ci gaba da kai kayyakin agaji na abin da magunguna ga al’umma kasar.