Assalamu alaikum masu karatu, barkammu da sake haduwa daku a wannan makon wanda shine mako na farko a cikin azumi watan Ramadan shirin na mu mai farin jini da albarka na Girki Adon.
A yau shafin na mu zaizo muku da kayataccun Girke Girke na azumi:
- Kasar Philippines Za Ta Dandana Kudarta Game Da Gudummawar Soja Da Amurka Ta Ba Ta
- CBN Ya Umarci Daraktocin Bankuna Su Mayar Da Bashin Da Suka Karba Ko Su Yi Murabus
Kamar yadda muka sani azumi lokaci ne na girke girke da dama, kuma lokaci da ya kamata uwargida ta tanaji kala kalar abinci da ya kamata ta rika yi ko kuma nace tasan mai maigida yafi bukata lokacin buda baki da kuma lokacin sahur, sannan lokaci ne na kirkirar kala kalar abunci don burge maigida.
Lokacin buda baki anaso mai azumin ya fara buda baki da Dabino saboda sunnah ne dashi akace a fara amma bawai dole bane, sai kayan marmari (Fruit) kamar kankana da lemo, gwanda, abarba, da dai sauransu. Bayan wadannan ba,aso mai azumi ya fara da sanyi wato ruwan sanyi sai kiga wasu sunfara da ruwan sanyi to gaskiya yana kawo kullewar ciki, anaso mai azumi ya fara da abu mai dan dumi dumi kamar shayi ko kunu ko kuma ruwan kanwa saboda kullewar ciki ko kuma kasala da ciwon ciki dan saboda mutum ya samu damar yin sallar tarawi.
Mene ne ruwan kanwa?
Ruwan kanwa wani ruwa ne da akeyiwa mai azumi yanada dadi sosai sannan idan mai azumi ya sha bayasa kasala yana warware cikin ko hanji cikin mutum zance, idan mai azumi yasaba da shan ruwan kanwa duk randa baisha ba bazai taba jin dadi ba.
Ya ake ruwan kanwa?
Da farko za ki samu gero sai a surfashi a cire masa dusa sannan a wankeshi a shanyashi yasha iska wato ya bushe sosai sai kidan soyashi yayi kanshi haka sannan ki zuba masa kayan kamshi citta, kanunfari, musuru, saiki bayar a nikamiki shi yayi laushi sosai kamar na kunu kizo ki shanyashi ya bushe sai ki ajiyeshi duk idan zaki dama saiki diba ki zuba a wani dan bokiti haka sai ki damashi da dan ruwan kanwa dama kin dora ruwa a wuta kamar de yadda zakiyi kunu idan ruwa ya tafasa saiki kashe shi kidan barshi yasha iska saboda karyazama kunu saiki zuba sannan ki zuba can suga haka saiki ajiyeshi haka ake shanshi da dumi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp