A uzu billahi minas shaidanir rajim. Bismillahir rahmanir Rahim. Allahumma salli ala Sayyidina Muhammadin alfatihi lima uglik; wal khatimi lima sabak; nasiril hakki bil-hakk; wal hadiy ila siradikal mustakimi wa ala alihi hakka kadrihi wa mikdarihil azim. Wa radiyyallahu an as’habi Rasulillahi sallallahu alaihi wa sallam. Wa la haula wa la kuwwata illa billahil aliyyil azim.
Karatunmu na wannan makon a cikin Littafin Ashafa, Fasali na tara, zai yi bayani cikin abin da Suratul Fat’hi ta tattare na daga girmame-girmamen Annabi (SAW) wanda Allah ya yi masa. Wannan sura ta fadi girman Annabi (SAW) da yawa saboda ta sauka bayan an hana Annabi shiga Makka. Lokacin da ya zo (daga Madina) zai yi umura mutanen Makka suka hana shi shiga, sai Manzon Allah ya yanka hadayarsa, abubuwa dai marasa dadi sun faru amma Annabi (SAW) ya yi hakuri ya dawo gida (Madina). Duk mutum idan ya yi hakuri a kan abu zai ga sakamako daga Allah, to a kan hanyar dawowa ana tafiya; Allah ya saukar da wannan surah. Annabi (SAW) ya yi bushara da ita.
- An Kaddamar Da Dandalin Bunkasa Noma Da Yaki Da Fatara Na Sin Da Afirka A Kenya
- ‘Yansanda Sun Cafke ‘Yan Uwan Da Suka Birne Matashi Da Ransa A Kaduna
Allah Ubangiji Madaukakin Sarki ya fada a cikin surar cewa, “Mu ne (kalma rabbaniyya) muka yi budi a gare ka budi mabayyani”. Kowa ya kalli Annabi SAW ya san wannan alheri ne daga Allah. Duk wannan abubuwa da Allah ya ba Annabi (SAW) su ne har yau Musulmi suke kai, kowa ya sani sai dai mutum ya yi musu hassada. Ba wata jama’a da suke kan alkhairi mai tsafta wanda ko mutum ya rikice idan ya kalli Musulmi ya san wadannan su ne ke kan tafarki madaidaici. Masu bata Musulunci da rikici ba za su cuci Musulunci da komai ba saboda addinin ba shi da wata boyayyar manufa wanda wani bai sani ba. Duk kafiran ma sun dage suna karanta karatuttuka na addinin saboda suna da kudi da kayan aiki, su ne ma suke fassara abubuwa na addinin don haka (masu hankalin cikinsu) sun san masu bata Musulunci daga su ne ba daga addinin ba. Mun gode Allah.
Allah ya yi wa Manzon Allah (SAW) budi kala-kala. Wani wajen ya ce ya yi masa “Budi Makusanci”, wani wurin Allah ya ce “Budi Mabayyani”, a surar Iza ja’a kuma, Allah ya ce ya yi masa “Budi A Sake (babu kaidi wato dabaibayi)”. Wannan shi ne budi mudlaki.
Kamar yadda ya zo a Suratul Fat’hi, Allah ya ce ya yi wa Manzon Allah Budi Mabayyani domin ya gafarta masa abin da ya gabata (na barin tarku aula) da zunubinsa (yadda ya dace da Annabi SAW) da abin da ya jinkirta (komai ya yi; in da ya yin ma, to an gafarta masa). Haka nan ko da ma zai yi wani abu a gaba shi ma an yafe masa (SAW), wannan idan ba Annabi (SAW) ba wa ya isa? Sannan Allah ya ce zai cika ni’imarsa a gare shi kuma ya shigar da shi tafarki madaidaici. Allah kuma ya ce zai taimake shi (SAW) da taimako mabuwayi. Allah shi ne wannan da ya saukar da natsuwa a cikin zukatan Muminai don su kara imani tare da imanin nasu (duk da imanin da mutum yake kai, akwai abin da zai gani sai ya ji ya kara masa imani, akwai maganar da zai ji sai ya ji ya kara samun tabbaci a zuciyarsa). Allah ya ce rundunar sama da kasa duk tasa ce. Allah masani ne kuma gwani.
Duk abin da ka ga Allah ya shirya akwai wata hikima a ciki, akwai wani abu da Allah ya yi niyya zai zartas a kansa. Allah ya yi haka ne don ya shigar da Muminai maza da Muminai mata cikin aljannatu wadda koramai ke gudana a karkashinta; za su dawwama a cikinta. Allah zai yafe musu; ya kankare musu zunubansu (ba wai shiga aljanna sai mutumin da ba shi da zunubi kwata-kwata ba ne, a’a, idan haka ne dukkanmu wa zai same ta? Falalar Allah dai idan mutum ya yi laifin ya san ya yi sai ya tubar wa. Allah kuma zai gafarta masa sai ya shiga). Allah yana yafe wa mutum dukkan zunubansa kuma ya shigar da shi aljanna; wannan rabo ne babba. Sannan wannan abu (na hana Annabi SAW shiga Makka) ya faru ne don Allah ya azabtar da Munafukai maza da Munafukai mata da Kafirai maza da Kafirai mata masu mummunar zato ga Allah. Don haka ba a so mutum ya dinga yi wa Allah mummunan zato. Shi ya sa ake so mutum ya tabbatar a cikin zuciyarsa cewa Allah ya shirya masa alheri ne.
Allah bai halicce mu don ya halaka mu ko don ya wulakanta mu ba. Allah Mahalicci ne, Mawadaci ne, wani zunubin za mu ga mun sha wuya; to ba don mun san da wuyar ba ai sharholiya da zunuban da za mu rika aikatawa ba za su yi kusa da tsafta ba. Don haka Allah yake ladabtar da mu, kamar dai yadda mutum yake ladabtar da dansa har ya san idan ya aikata wani abu zai sha bulala, za ka ga yana kiyayewa. Don haka mutum ya dinga kiyayewa, ya yi kyakkyawan zato ga Allah, ka dinga aikata alheri; idan ka ga Allah ya zubo ma wani abu ka yi hakuri ka san cewa rahama ce. Idan ka ga mutum ya dama madaci ko ya dama batsarmama ko duk wani abu mai daci ya dura wa dansa ai ba so yake ya wahalar da shi ba, sauki ne yake nema masa, lafiya yake so ya samu. Idan aka ga an yanke wa mutum kafa ko hannu wannan bala’i ne amma kuma lafiya ake nema masa shi ya sa aka yanke don idan aka bari sai ciwon ya harbi wata gabar har ta je ta harbo wani wurin da ba za a iya datsewa ba kamar misali wuya, ka ga nan sai mutuwa. Don haka idan mutum ya ga wata jarabta daga Allah to ya tabbatar magani ne Allah yake masa sai ya yi hakuri. Shi ya sa Shehu Ibrahim Inyass (RTA) ya ce da Dan Adam ya san waye Allah Arrahmanu duk sharri idan ya same shi sai ya karba yana dariya, don ya san alheri yana nan tafe.
Don haka masu mummunan zato ga Allah, kewayon mummuna zai tabbata a kansu, domin shi Allah alheri ne yake zuwa daga wurinsa da’iman. Su wadannan masu mummunan zato ga Allah; Allah ya yi fushi a gare su, ya nesanta su daga rahamarsa kuma ya tanadar musu wutar jahannama, makoma ta yi muni idan ta zamo jahannama. Rundunar sama da rundunar kasa duk ta Allah ce. Allah Mabuwayi ne kuma Gwani.
Wasu za su iya cewa, idan rundunar sama da kasa duk ta Allah ce to ya saukar da ita mana a wannan lokacin, ga Musulmi nan irin su Falasdinawa suna shan wuya, kaza da kaza. To a nan, malamai sun ce a wancan lokacin da Allah ya saukar da rundunarsa babu mutane ne da yawa. Annabi (SAW) da rundunarsa ta Sahabbai duk ba su wuce su dubu uku ba (a Fatahu Makkata ne suka kai yawan dubu goma), a karshen wani yaki ko Tabuka ne, shi ne aka kai yawan dubu talatin. To amma yanzu mu Musulmi a duniya mun haura Biliyan daya, idan wannan Biliyan din za ta hadu sai an sauko mata da wata runduna daga sama kuma? Shi ya sa yanzu babu wata runduna mai sauka, idan za ku tashi ku yi wa kanku magani ku yi. Yanzu misali idan mutum Biliyan suka taru, kowa a cikinsu zai iya yakar mutum uku, idan aka yi wannan haduwa ai ba sai an saukar da wata runduna daga sama ba. Amma dai kuma har yau taimako na Allah yana nan.
Allah ya ce wa Manzon Allah (SAW) “Mu muka aiko ka (ya Rasulallahi a matsayin) mai shaida (ga al’ummarka) kuma mai bushara, sannan mai gargadi (Sai ya zamo tun daga kan Annabin da duk al’ummarsa) ku yi imani da Allah da Ma’aikinsa. Kuma ku girmama shi sannan ku girmama shi dai. Ku yi tasbihi ga Allah; safe da maraice. Ka ga wadannan da suke mubaya’a da kai; da Allah suka yi (mubaya’ar), Hannun Allah ne a kan nasu (yadda ya dace da Allah). Duk wanda ya warware wannan mubaya’a; kansa ya warware wa (kai dai ya Rasullallahi Allah zai taimake ka). Duk wanda ya cika wa Allah abin da ya yi alkawari, Allah zai ba shi lada mai girma”.
Wadannan ayoyi tun daga farkon surar ta Fat’hi har zuwa wurin da Allah ya ce masu mubaya’a da Annabi sun yi ne da Hannun Allah (yadda ya dace da shi SWT); sun kunshi bayani ne a kan fifikon Annabi (SAW) da kirari gare shi da bayyana girman matsayi da darajarsa a wurin Allah. Da irin ni’imar da Allah ya yi a gare shi (SAW) da abin da siffantawa ma zai zama takaitawa ne a gare shi (SAW) – ballantana ma a ce wani ya kai karshe har ya ketare iyaka.