Gobara ta kone Shagunan 150 a babbar kasuwar Kachako da ke cikin karamar hukumar Takai a jihar Kano.
Kakakin yada labarai na hukumar kashe gobara na jihar Alhaji Saminu Abdullahi, ya tabbatar da afkuwar iftila’in, inda ya ce, lamarin ya faru ne a yammacin ranar litinin.
Saminu ya ce, ” Mun samu kiran waya na gaggawa daga sashen ofishin hukumar da ke Takai da misalin karfe 01:13, inda muka tura jami’an mu zuwa kasuwar don dakile yaduwar ta zuwa sauran shagunan da ke kasuwar”.
Ya ce, jami’an sun yi nasara wajen kashe ta tare da kubutar da kimanin shaguna 800.
Shugaban ya ci gaba da cewa, ana zargin wasu masu shan sigari ne suka haddasa tashin ta.
A wata hira da aka yi da kakakin hukumar musamman akan yawan samun tashin gobara a jihar, ya danganta hakan akan yanayin hunturu da ake ciki a yanzu, inda ya gargadi jama’a da su dinga kiyaye wa da yadda suke yin amfani da wuta tare da kashe dukkan kayan wutar lantarki a yayin barcin dare.