Sama da shaguna 50 ne suka kone yayin da dukiya ta miliyoyin Nairori suka lalace a wata gobara da ta tashi a kasuwar Yan Katako da ke unguwar Rijiyar Lemu a karamar hukumar Fagge a jihar Kano.
Shugaban kasuwar, Mamuda Abdullahi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana cewa gobarar ta tashi ne da misalin karfe 1 na daren ranar Litinin, 26 ga watan Fabrairu.
Shugaban ya yabawa jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Kano bisa gaggawa da suka yi, yayin da ya yi kira ga gwamnatin jihar da masu hannu da shuni da su tallafa wa ‘yan kasuwar da suka yi asarar dukiyarsu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp