Da safiyar yau Talata ne gobara ta tashi a kasuwar saida kayan masarufi da ke Kano da aka fi sani da kasuwar Singa (mawaka) da ke matsuguni a cikin tsakiyar Kano.
Har yanzu yanzu dai ba a gano hakikanin musabbabin gobarar ba, sai dai gobarar na zuwa ne kasa da kwanaki biyar da irin wannan gobarar ta tashi a kasuwar Badume tare da yin barna sosai.
Ganau sun shaida cewar jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Kano sun yi iya kokarinsu wajen kashe gobarar tare da rage barnarsa.
Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin ga wakilinmu, jami’in watsa labarai na hukumar ‘yan kwana-kwana ta jihar Kano, Malam Saminu Yusuf Abdullahi, ya ce wutar ta fara ci ne da safiyar ranar Talata kuma ta lakume kayan masarufi da suka kunshi biski, minti, cingom, da sauran kayayyaki tare da ruguza wani begi guda.
Abdullahi, ya ce, jami’ansa sun yi kokari sosai wajen shawo kan wutar.
Ya ce zuwa hada wannan rahoton babu asarar rai ko daya sakamakon wannan gobarar.