Ministan Sufuri, Said Alkali ya ce, layin dogo na Nijeriya zai fara sayar da tikitin shiga jirgin kasan ta yanar gizo a ranar Laraba.
Alkali ya bayyana haka ne a ranar Litinin a Abuja yayin bikin kaddamar da sayar da tikitin shiga jirgin ta yanar gizo na hanyar Legas zuwa Ibadan da Itakpe zuwa Warri. A cewarsa, tsarin sayar da tikitin ta yanar gizo, kudin shigar zai tafi kai tsaya zuwa asusun tattara harajin gwamnati.
- Rikicin Gaza Ya Haifar Da Rashin Tabbas a Kasuwar Mai ta Duniya
- Tagwayen Da Aka Haifa Manne A Kano Sun Tashi Zuwa Saudiyya Domin Raba Su
Ya kuma kara da cewa, tsarin bayar da tikitin zai rage yawan cin hanci da rashawa da kuma tabarbarewar kudaden shiga.
“Hakanan zai taimaka wajen tabbatar da tsaron fasinjojinmu da kuma kaucewa cin hanci da rashawa. Burin wannan gwamnati shi ne, kawar da cin hanci da rashawa.” inji shi.