Ma’aikatar ilimi ta jihar Kano ta ayyana gobe Litinin a matsayin ranar da za’a ci gaba da karatu a makarantun firamare da sakandire na gwamnati da masu zaman kansu da na kwana a jihar.
Hakan na kunshe ne acikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun daraktan fadakarwa na ma’aikatar da aka rabawa manema labarai a jihar.
Sanarwar ta kara da cewa a gobe 9 ga watan Janairu ne za a koma makarantun jeka ka dawo da daliban kwana.
Yayin da yake nuna jin dadinsa kan hadin kai da goyon bayan da ake baiwa ma’aikatar, kwamishinan, Rt Hon Ya’u Abdullahi Yan’shana ya bukaci iyaye/masu kula da dalibai da dalibai da su tabbatar da bin doka da ka’idojin da aka gindaya wurin komawa ajujuwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp