Gwamnatin tarayya ta gargadi ma’aikatanta cewa, duk ma’aikacin da ba a tantance bayanansa a sabon tsarin biyan ma’aikatan gwamnatin tarayya albashi (IPPIS) ba da ake yi yanzun zuwa karshen mako ba, za a cire shi daga cikin ma’aikatan da gwamnati ke biya albashi.
Daraktan yada labarai na ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya, Mohammed Ahmed, a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Laraba, ya ce atisayen na tsawon mako biyu wanda zai kare a ranar Juma’a, 27 ga Oktoba, 2023., an shirya shi ne musamman don tantance bayanan ma’aikatan da ba su shiga tsarin ba a baya.
- Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Fika Ya Rasu Yana Da Shekara 90
- Malamar Jami’ar Nasarawa Da Aka Sace Ta Kubuta
Ahmed ya ce, gwamnatin tarayya ta fara aiwatar da tsarin IPPIS ne a shekarar 2007 don tabbatar da gaskiya, daidaito da kuma aminci wajen gudanar da bayanan ma’aikata, tare da rage yawan kudaden da ake kashe wa ma’aikatan.
A cewarsa, sakamakon kokarin da gwamnati ke yi na dakile wa da bankado ma’aikatan bogi da kuma rage yawan kudaden da ake kashe wa ma’aikatan, tsarin IPPIS ya fi mayar da hankali kan biyan albashi maimakon bangaren harkokin gudanarwar ma’aikata.