An bayyana gogewar kasar Sin a fannonin ilimi da binciken kimiyya da samar da fasahohin da ake amfani da su a cikin gida, a matsayin abun karfafa gwiwa ga kasashen Larabawa, domin suna da burin koyo da amfani da fasahohi irin na kasar Sin.
Shugaban kungiyar kawancen kasashen Larabawa kan ilimi da binciken kimiyya (Arutic), Mohamed Abdel Fattah Moustafa ne ya bayyana haka, yayin hirarsa ta baya-bayan nan da kamfanin dillancin labarai na Xinhua.
A cewarsa, ilimi da binciken kimiyya da fasahohin na amfanin cikin gida, bangarori ne da kasashen Larabawa suke sha’awa a shekarun baya-bayan nan, ta hanyar hadin gwiwa da sauran kasashe, musamman kasar Sin.
Ya ce ya yi imanin cewa, kyautatuwar dangantaka tsakanin Sin da kasashen Larabawa na da nasaba da yadda kasashen suka fahimci cewa, kasar Sin aminitacciya ce.
Bugu da kari, ya ce taimakon da Sin ke ba kasashe masu tasowa ta hanyar hadin gwiwa a bangarorin ilimi da binciken kimiyya da fasaha, zai taimaka wajen kirkiro wani sabon kawancen kasa da kasa da haifar da moriya ta bai daya da musaya. (Fa’iza Mustapha)