Gwamnatin Jihar Gombe ta amince da kashe naira biliyan 1 da miliyan 149 don gudanar da ayyukan sanya fitilun hanya masu aiki da hasken rana da sauran muhimman ababen more rayuwa a fadin kananan hukumomi uku na jihar.
An amince da ayyukan ne a yayin taron hukumar kula da ayyukan hadin gwiwa (JPC) karo na 5, wanda Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya jagoranta.
- Dole Gwamnatin Tarayyar Nijeriya Ta Daina Barazana Ga Masu Sukar Ta – Amnesty
- Fadin Yankin Da Ke Fama Da Zaizayar Kasa Na Kasar Sin Ya Ragu A 2024
Da yake jawabi yayin ganawa da manema labarai bayan taron, babban daraktan hukumar kula da ayyukan hadin gwiwan, Dakta Mahmood Yusuf, ya bayyana cewa majalisar ta amince da ayyuka uku wadanda za a gudanar a wasu kananan hukumomi uku don bunkasa ayyukan more rayuwa daidai da manufar gwamnatin jihar.
Ya ce ayyuka ukun sun hada da sanya fitilun hanya masu aiki da hasken rana a sabbin hanyoyin da aka gina a Kumo shalkwatar karamar hukumar Akko da kewaye kasuwar NALDA da samar da fitilun hanya masu aiki da hasken rana a cikin kasuwar da ke gundumar Kwadon a karamar hukumar Yamaltu/Deba da kuma fadada kasuwar hatsi da gina ban-dakunan guda 6 a karamar hukumar Billiri.
A nasa jawabin shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomi ALGON na Jihar Gombe, Barista Sani Ahmad Haruna, ya bayyana cewa majalisar ta lura da yadda ake samun yawaitar sata a gine-ginen gwamnati, da suka hada da makarantu da makabartu, da dai sauransu.
Ya sanar cewa karamar hukumar ta kuduri aniyar daukar tsauraran matakai don dakile wannan barazana ta hanyar tura jami’an GOSTEC da Operation Hattara don inganta tsaro.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp