• English
  • Business News
Tuesday, October 28, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Goron Barka Da Shiga Sabuwar Shekarar 2024 Daga Jawabin Shugaban kasar Sin

by CGTN Hausa
2 years ago
Sin

Kwarin gwiwar da shugaban kasar Sin, Xi Jinping ya bai wa al’ummar kasarsa a jawabin da ya gabatar na maraba da sabuwar shekarar miladiyya ta 2024, ya nuna irin yadda Sinawa da shugabanninsu suka zama tsintsiya madaurinki daya da tara karfi wuri guda wajen ciyar da kasarsu gaba. 

Kamar yadda shugaban kasar ya nuna, kowa ba a raina kokarin da ya yi ba wajen bayar da gudunmawa ga samun nasarar abubuwan da kasar ta cimmawa a shekarar 2023. “Dukkanku, tun daga manoma a gonaki zuwa ma’aikata a kan benayen masana’antu, daga ‘yan kasuwa zuwa ma’aikatan da ke gadin kasarmu–hakika, mutane daga kowane bangare na rayuwa – kun yi kokarinku. Kowane dan kasar Sin ya ba da gudummawa mai ban mamaki! Har kullum al’ummar Sinawa, abin dogara ne wajen jure wahalhalu.”

  • Sin Ta Mai Da Hankali Ga Kimiyya Da Fasaha
  • Shugabannin Sin Sun Kalli Wasan Gargajiya Na Opera Domin Maraba Da Sabuwar Shekarar 2024

Ga duk wanda ya san Sinawa, ya san mutane ne masu aiki tukuru da nuna kishin kasa. Kamar yadda Shugaba Xi ya ayyana, duk da cewa, shekarar 2023 ta zo da ibtila’i kamar ambaliyar ruwa da girgizar kasa, amma kuma akwai abubuwa da aka samu nasara a kansu a zahiri, “za mu tuna wannan shekarar a matsayin daya daga cikin shekarun aiki tukuru da juriyar hakuri. Daga yanzu, muna da kwarin gwiwar gaba za ta fi kyau.”

A shekarar da aka yi ban kwana da ita, kasar Sin ta samu ci gaba mai inganci, inda aka bude wani sabon babi na farfado da yankunan karkara da yankin arewa maso gabashin kasar. Saurin ci gaban sabon yankin Xiong’an ya wuce yadda ake tsammani, kuma yankin tattalin arziki na kogin Yangtze ya bunkasa yayin da babban yankin Greater Bay na Guangdong, Hong Kong da Macao ya ba da jagora wajen samun ci gaba. Kasar Sin ta kara karfin tattalin arzikinta duk da matsaloli da dama da aka fuskanta.

Wani abu mai muhimmanci kan ci gaban Sin da shugaba Xi ya tabo a jawabin nasa shi ne batun kirkire-kirkiren fasaha wanda ya ba da misali da ci gaban da aka samu wajen fara sayar da dankareren sabon jirgin saman da kasar ta kera na C919, sannan babban jirgin ruwan da kasar ta kera ya kammala balaguron gwaji, kana ’yan sama jannati na Shenzhou na ci gaba da binciken da suke yi a sararin samaniya. Bugu da kari yadda kayan da Sin ke kerawa da ake ya yi kamar sabbin wayoyin hannu na zamani, motoci masu amfani da sabon makamashi manuniya ce a kan kwarewar masana’antun kasar.

LABARAI MASU NASABA

An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka

Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani

Irin wannan ci gaba da Sin ke samu ba abin mamaki ba ne ga duk mai bibiyar tarihinta, domin kasa ce da take da tsari na wayewa tun fil azal, kuma ba ta yarda ta sauka daga kan layi ba. Kayan tarihin da aka gano a yankin Liangzhu da Erlitou sun kara fayyace abubuwa da yawa game da wayewar kasar Sin wanda Shugaba Xi ya ce shi ne sirrin kwarin gwiwarsu.

Kasancewar Sin kasa ta biyu a duniya wajen ci gaban tattalin arziki, Shugaba Xi ya ce ta sauke nauyin dake wuyanta. Ta gudanar da tarurruka daban-daban na hadin gwiwa da difilomasiyya a yankin Asiya, Afirka da sauran sassan duniya.

Kasar ta sha nanata bukatar kawo karshen mummunan yakin da ake gwabzawa a yankin Gaza tsakanin Hamas da Isra’ila ba kawai da fatar baki ba, amma a aikace kamar yadda ta rika kada kuri’a kan haka a zauren Majalisar Dinkin Duniya. Haka nan, ziyarar da Shugaba Xi ya kai Amurka kwanan baya da yadda manya da hamshakan Amurkawa suka rika kai ziyara Beijing a shekarar 2023, ya nuna aniyar kasar ta samar da duniya mai cike da zaman lafiya da cin moriyar juna. Ina iya tunawa, Shugaba Xi ya ce bai kamata gasa da juna ta fuskar ci gaba ta rikide ta zama kiyayya ba, a ganawarsa da Shugaba Joe Biden a birnin San Francisco.

Da yake Sin na cika shekara 75 da kafuwa a matsayin Jamhuriya a sabuwar shekarar da aka shiga, burin da Shugaba Xi ya bayyana a jawabinsa na samar da ingantacciyar rayuwa ga al’ummar kasa ta yadda yaran kasar za su samu ingantaccen ilimi, matasa su samu damar gudanar da sana’o’insu da samun nasarar abubuwan da suke fatan zama a rayuwa, da kula da dattawa da sauran harkoki da za su kyautata rayuwar al’umma, ya zama babban albishir ba ga Sinawa ba kadai har da sauran kawayenta musamman na Afirka da take taimakonsu su tsaya da kafafunsu.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka
Daga Birnin Sin

An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka

October 27, 2025
Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani
Daga Birnin Sin

Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani

October 27, 2025
Ribar Manyan Masana’antun Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.2 Cikin Dari A Watanni Tara Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

Ribar Manyan Masana’antun Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.2 Cikin Dari A Watanni Tara Na Farkon Bana

October 27, 2025
Next Post
Hare-Hare: Gwamnatin Filato Ta Ayyana Zaman Makokin Mako Guda

Hare-Hare: Gwamnatin Filato Ta Ayyana Zaman Makokin Mako Guda

LABARAI MASU NASABA

gaza

Majalisar Dattawa Ta Maido Da Ranar Tantance Sabbin Shugabannin Sojoji Zuwa Laraba

October 28, 2025
Duk Da Barazanar Tattalin Arzikin Duniya, Kasar Sin Ta Sanya Tabbaci Da Kwanciyar Hankali A Duniyarmu Mai Cike Da Ruɗani

Duk Da Barazanar Tattalin Arzikin Duniya, Kasar Sin Ta Sanya Tabbaci Da Kwanciyar Hankali A Duniyarmu Mai Cike Da Ruɗani

October 28, 2025
Ina Fatan Buga Kofin Duniya Na 2026 — Messi

Ina Fatan Buga Kofin Duniya Na 2026 — Messi

October 28, 2025
Tsohon Kwamishina Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Sayar Da Filin Makaranta Kan Miliyan 100

Tsohon Kwamishina Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Sayar Da Filin Makaranta Kan Miliyan 100

October 28, 2025
An Matsa Min Sai Na Koma Jam’iyyar APC – Gwamnan Filato

An Matsa Min Sai Na Koma Jam’iyyar APC – Gwamnan Filato

October 28, 2025
’Yansanda Sun Ƙaryata Rahoton Ƙone Gidan Shugaban Jam’iyyar PDP A Bauchi

’Yansanda Sun Ƙaryata Rahoton Ƙone Gidan Shugaban Jam’iyyar PDP A Bauchi

October 28, 2025
Mutum 18 Sun Mutu, 40 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Kebbi 

An Kashe Mutum 10 A Harin Ramuwar Gayya A Jihar Kebbi

October 28, 2025
Ganduje Na Kara Shan Matsin Lamba A Kan Ya Sauka

Zargin Almundahana: An Ɗage Shari’ar  Ganduje Da Matarsa Saboda Rashin Miƙa Takardu

October 28, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

Sojoji Sun Kashe Masu Yi Wa ISWAP 4 Safarar Makamai A Borno

October 28, 2025
Sin

APC Ta Yi Barazanar Dakatar Duk Kwamishinan Da Bai Sanya Irin Hular Tinubu Ba

October 27, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.