Barkanku da kasancewa tare da shafin GORON JUMA’A shafin dake bawa kowa damar mika sakon gaishe-gaishensa zuwa ga ‘yan’uwa da abokan arziki, na kusa dana nesa har ma da wadanda aka dade ba a hadu ba.
Kamar kowane mako yau ma shafin na tafe da wasu sakonnin gaishe-gaishen da ku ka aiko mana, inda sakon farko ya fara da cewa;
Sako Daga Zainab Muhammad Jihar Katsina
Ina gaida Mahaifiyata da mahaifina sai ‘yan uwana Hauwa’u, Fatima, Nana, Sa’ad, Maimunatu, sannan kawayena, Zainab Garba, Aisha Kabir, Sadiyya Imran, da fatan sun yi Juma’a lafiya.
Asiya Isah Jihar Kaduna
Ina gaiahe da Babbar kawata wato Hadiza Bello Sule, Mahmah, Maryam Sani, Hafsatu Dahiru, Shamsiyya Dahiru, Khadija Dauda, Maijidda Yusuf, Fatima Musbahu, Zaliya Hassan, Fatima Hassan, Junaidiyya Hassan, Ummi Ibrahim, Rahina Salisu, Lawisa, da dai sauransu da fatan sun yi Juma a lafiya.
Sako daga Yusuf Lawan Jihar Jigawa
Ina so a gaishe mun da; Malaman makarantarmu kamar su Mal. Iliyasu, Mal. Nura, Mal. Mukhtar, Malama Hafsa, Malama Firdausi, Malama Sadiya, Malama Sakina, sai abokaina Aliyu, Adam, Shamsu, Walid, Sani, Kamis, Zubairu da fatan sun yi juma a lafiya.
Sako Daga Rahma Wakili Jihar Zamfara
Ina gaishe da Mamana da Babana, da yayye da kannena Fati, Rukayya, Hafiz, Faruk, Usman, Yaya Nafi, Aisha, sai kanwar kawar makociyar ‘yar yayan kakan kishiyar surukar kanwata Hajiya Zubaida Zubairu Zukanya, da fatan sun yi Juma’a lafiya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp