Jama’a barkanku da juma’a, barkanku da kasancewa tare da wannan shafi na Goron Juma’a. Shafin da ke bawa kowa damar mika sakon gaishe-gaishensa zuwa ga ‘yan uwa da abokan arziki na kusa, da na nesa. A yau ma ina dauke da wasu sakonnin gaishe-gaishen, sai dai kuma kafin na je ga sakonnin masu karatu da suka aiko, sai na fara mika tawa gaisuwar zuwa ga dukkanin ma’aikatan wannan gidan jarida mai albarka ta LEADERSHIP HAUSA, musamman Editana Abdulrazak Yahuza Jere, da sauran al’ummar musulmi baki daya, da fatan an yi sallar juma’a lafiya, kuma da fatan an yi kwalliyar juma’a tare da kai ziyara lafiya. Sai sakonnin da kuka aiko kamar haka:
Sako daga Hafsat Sa’eed:
Assalamu alaikum al’umar musulmai baki daya, ina yiwa kowa da kowa Barka da Jumma’a, musamman ma iyayen gidana a siyasa Abubakar da kuma Uwar Dakina Uwar Marayun Jihar Kebbi, Hajiya Fatima Abubakar Malami San da kuma Hon. Abubakar Umar Jarengol da Masanin Mayobani da kuma Hon. Kwacham buba Abdurahaman da dai sauran jama’ar da ban ambata ba, don ba za su kirguba, ina yima kowa da kowa Barka da Jumma’a, Allah ya maimaita mana ya sa muga na badi haka da rai da lafiya.
Sunana Yakubu Bala Gwamaja: Ina gaida masoya Annabi Muhammad (S.a.w) baki daya, ina mana Barka da Jumma’a, Musaman Alhaji Bala Baba Mai Gidaje ‘Family’s’ da Gandun Masaka ‘Family’s’ da Malam Baban A’i ‘Family’s’ da Mijin Yawa ‘Family’s’ da ‘Yan uwana ‘yan Kannywood, da ‘Yan uwana ‘Yan kantin Kwari da dukkan mutanan Gwammaja da Masoya na ko ina da na Makarantar GSS Dala, da na ‘Ligal Law Dip’.
Sako daga Safiyya Mustapha Mu’az:
Ina gaida mahaifina Malam Mustapha mu’az Gurin Gawa da mahaifiyata Rahama Rabi u Gurin Gawa da Antina Rabi’at Sidi Bala da Babban yayana Usama Sidi Bala, da ‘yar uwata Ummi Mustapha Mu’az Gurin Gawa (Maman Abdallah) da Maryam Mustapha Mu’az da dan uwana Hassan Mustapha mu’az da Aminiyata Sadiya Bashir Gurin Gawa da kawata Khadija Muhammad Fulani da Malam Abba bako Gano, Abdullahi Sabo Dan Agundi, Usam Abdulmaliki (na ‘yan baro) Dawakin Kudu Da shafa’atu Shehu Bello Gurin Gawa da Hayatu Isyaku.
Sako daga Khausar Salis (Aglan Nissah) daga kasar Nijer:
Ina mika sakon gaisuwa da Barka da Jumma’a zuwa ga daukacin musulmin duniya baki daya musaman ‘yan uwa da abokanan arziki na nesa Haseenatou Autar Manya alkhairin Allah ya kai miki har gadon bacci, Fauzeeya Idris Namadi, Jamila Umar Janafti kakata rabbi ya jibanci lamarinki ina miki fatan alkhairi a duk inda kike, Safna Aliyu Jawabi gaisuwa ta musamman gareki, Hajjiya Maryam Sakatare ba zan manta dake ba ina miki gaisuwar ban girma, Rabi’at Sidi Bala kiji dadinki ta wajena ina fatan kin Sallata lafiya, Yayana Muhammad Kareem ina mika gaisuwa tun daga nan kasar Niger har izuwa Nijeriya, kai kowa da kowa duk ina gaishe ku, Allah ya karbi ibadunmu Ameen.
Sako daga Muhammad Karim daga garin Kaduna:
Ina gaishe da Fatima Ibrahim Khalil, Asmeemat Zeeyan, Salahuddeen Muhammad, Nazifi Yarima, Fateemah Kankia, Khausar Salis, Hafsat Ibrahim Khalil, Dakta Maryama, Ibrahim, Umar Dayyan, Azizat Hamza, Meerah Y Turaki, Jamila Musa, Jamila Umar (Janafty), Sanaz deeya, Farida Musa (Sweery), Comrade Sani Musa Daitu da Hannah Mahmud.