Jama’a barkammu da juma’a, barkanku da kasancewa tare da wannan shafi na Goron juma’a.
Shafin da ke bawa kowa da kowa damar mika sakon gaishe- gashensa zuwa ga ‘yan uwa da abokan arziki na kusa da na nesa. A yau ma ina dauke da wasu sakonnin gaishe-gaishen, sai dai kuma kafin na je ga sakonnin masu karatu da suka aiko, sai na fara da mika tawa gaisuwar zuwa ga dukkannin ma’aikatan wannan gidan jarida mai albarka ta LEADERSHIP HAUSA, musamman ma Editana Abdulrazak Yahuza Jere, da fatan anyi sallar juma’a lafiya, kuma da fatan an yi kwalliyar juma,a tare da kaiziyara lafiya. Sai sakonnin da kuka aiko kamar haka.
Sako daga Nana Hauwa’u Idris
Assalamu alaikum, da fatan mun wayi gari cikin koshin safiyar Jumma’a babbar rana Allah ya bamu lada da albarkacin dake cikin ta, ya kawo mana sauki a halin rayuwar da muke fuskanta.
Ina gaida yayyena da suka hada da Sulaiman ,Muhammadu, Ummi, Aisha, Safiyya,da kuma Khalifa da fatan za su yi sallar Jumma’a cikin koshin lafiya
Sako daga Abba Abubakar (Kwara), Kano
Ina taya daukacin al’ummar musulmi na duniya baki-daya barka da sake zagayowar wannan rana ta Juma’a.
Da farko, ina mika sakon gaisuwata ga ‘yan’uwana da abokan arziki, musamman iyayena yayye da kuma kanne; kamar su Malam Uba, Saminu, Idi da kuma Auwalu Yellow.
Haka nan, kannena akwai Sabi’u Auta, Mujittapha indararo, Audu cin gafe, Sunusi father, Muttaka da kuma Bashir Dan kuturu.
Akwai kuma abokaina irin su Ya’u, Danhajjo, Habu, Shehu tariga,
Danshuni, Mamiyo, Alhaji Homes da sauransu.
A karshe, ina addu’ar Allah ya ji kan iyayenmu da kakanninmu da abokanmu da makwabtanmu da danginmu da yayye da kanne da sauran daukacin al’ummar musulmi baki-daya, amin.
Sako daga Saifuldeen Aliyu
Assalamu alaikum, ina yi wa kowa da kowa barka da juma’a. Ina mika gaisuwa na da fatan alheri zuwa ga mahifiyata Hajiya Daharatu Musa, da mahaifina Alhaji Aliyu Isah Dankyalta,da kannena Maryam da Isah Aliyu da Abdulrahman Aliyu da Aisha Ahmad Muhammed da kawu na Ishak Garba Bako da matarsa Amina Auwal Kila. Da fatan anyi sallar juma’a lafiya kuma ina muku barka da juma’a.